Wane hali Shugaba Buhari na Nigeria ke ciki?

An zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar hawainiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar hawainiya

Tun dai ranar 5 ga Fabrairun 2017, lokacin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rubuta wa Majalisar Dokokin kasar takardar neman tsawaita hutunsa, 'yan kasar ke ta tofa albarkacin bakinsu.

Babban mai ba wa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Femi Adesina, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa "shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Dokokin kasar takardar neman iznin karin hutu domin kammala wasu gwaje-gwaje da likitoci suka bukata."

Wannan ne kuma ya sanya Najeriya ta dauki dumi kan yanayin da shugaban yake ciki.

Dama dai kafin lokacin, jita-jitar mutuwar shugaban ta kauraye kasar, har ta kai ga jami'an gwamnati suka yi ta faman sanya hotunan Buhari tare da iyalansa ko kuma wasu manyan mutane.

Sai dai kuma wasu sun ta nuna shakku kan sahihancin hotunan bisa dalilan cewa hotunan sun kwana biyu.

An ta tafka muhara kan hakikanin cutar da ke damun Buhari amma daga bisani jami'an gwamnatin kasar sun ce ba wata cuta ce mai tsanani ba, ke damun shugaban.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai yi aiki tare da Trump domin karfafa dangantakar kasashen biyu

Ko tafiyar Buhari ta karya doka?

Kafin tafiyar shugaba Buhari dai, sai da ya mika wa mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ragamar mulkin kasar, a matsayin mukaddashi.

Hakan ne ma ya sa wasu lauyoyi suke ganin bai kamata 'yan Najeriya su tayar da hankalinsu ba kan tafiyar shugaban ko da kuwa ya tafi jiyya ne.

Dr. Aminu Gamawa wanda lauya ne a Najeriya, ya ce, "Na kalubalanci duk wani lauya a Najeriya da ke da tunanin tafiyar shugaban ta karya dokar kasa."

Ya ci gaba da cewa, "Babu wani sashen kundin tsarin mulki da aka yi wa karan tsaye saboda shugaba ya bai wa mataimakinsa mukaddashi."

Sai dai kuma wasu na da ra'ayin cewa duk da cewa babu wani tsarin mulki da aka taka, ya kamata shugaban ya yi wa 'yan kasa jawabi kan halin da yake ciki.

Ja'afar Ja'afar, wani marubuci a Najeriya na da irin wannan ra'ayi, a inda ya ce, "Kwarai babu wata doka da aka keta amma kuma ya kamata shugaban kasa ya yi wani dan jawabi da zai sa hankalin 'yan Najeriya ya kwanta."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zargi gwamnatin Shugaba Buhari da yin tafiyar hawainiya

Shin rashin lafiyar Buhari ta shafi 'yan Najeriya?

Akwai kuma wasu jami'an gwamnatin Najeriya da ke da ra'ayin cewa batun rashin lafiyar shugaban, ba abun da ya shafi 'yan kasar ba ne.

Sai wasu 'yan kasar sun mayar da martani cewa tun da dai shugaban Najeriya ne wanda ke jagorancin kowa da kowa, 'yan kasar sun cancanci sanin hakikanin halin da Buhari yake ciki.

Har wasu ma na cewa 'yan Najeriya na da hakkin sanin halin da shugabansu ke ciki kasancewar da kudaden kasar ake sama masa magani sannan kuma ofishin jakadancin Najeriya da ke Ingila, inda Buharin yake ciki, mallakar 'yan Najeriya ne.

Image caption Buhari ya ce marigayi Sultan Ibrahim Dasuki, ya yi aiki tukuru wajen hada kan 'yan Najeriya

Me ya sa Buhari ya fita waje domin neman magani?

'Yan Najeriya da dama na ganin rashin kyautawar shugaba Buhari kan fita kasashen waje domin neman lafiya.

Gwamnatin shugaban dai ta sha yin kira ga 'yan kasa wajen mayar da hankali kan tsayawa a asibotocin cikin gida, a duk lokacin da aka samu larura.

Wasu kuwa na alakanta rashin kyautawar shugaban, bisa dogaro da irin biliyoyin kudin da ake ware wa asibitin da ke fadar shugaban, a kasafin kudin 2016 da ma na 2017.

Sai dai kuma likitoci da masana harkar lafiya na cewa ba haka lamarin yake ba.

Farfesa Wali, shi ne babban mai duba lafiyar tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Babangida, ya ce, "Ba haka abin yake ba saboda mafi yawancin lokuta likitan shugaban ne ke ba da shawarar a fita waje, idan ya ga cutar ta fi karfin a magance ta a cikin gida."

Su wane ne suka gana da Buhari?

Ba ya ga iyalan shugaba Muhammadu Buhari, wani hoto da aka fitar a kafafen sada zumunta da ma sauran kafafen watsa labarai na kasar, an ga shugaban tare da tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Alhaji Bisi Akande.

Kuma a makon da ya gabata ne shugaban Majalisar Dattawan kasar, Bukola Saraki, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "Ina farin cikin sanar da ku cewa mun gana da shugaba Buhari kuma har ya yi min barkwanci kamar yadda ya saba, kan yadda nake gudanar da ayyukana da tsakar dare."

Shi ma shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya ce, ya tattauna da shugaba Buhari har tsawon minti biyar da daddaren ranar Larabar da ta gabata.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Kakakin, Turaki Hassan ya fitar, Dogara ya ce, "Duk da dai shugaban da kakakin Majalisar Wakilan sun tattauna kan wasu batutuwan da suka shafi kasar, mutanen biyu sun mayar da hankali kan yadda bangaren Zartarwa da Majalisa za su yi aiki tare wajen samar wa talakawa abinci."

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Najeriya za ta so kyautatuwar dangantakar da ta samu da Amurka ta dore a lokacin mulkin Donald Trump

A ranar Litinin ne kuma shugaban Amurka, Donald Trump, ya kira shugaba Buhari ta wayar tarho, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi tsaro.

Masu sharhi na ganin cewa abin da hakan yake nufi shi ne, shugaban Najeriya, Buhari na nan da ransa, sabanin tunanin da wasu ke yi cewa shugaban ya mutu.

Har wa yau, ana ganin rashin lafiyar da Buhari ke fama da ita, ba ta kai tsananin da wasu 'yan Najeriyar ke tsammani ba.

Yanzu haka dai abin da 'yan Najeriya ke jira su gani shi ne ranar da shugaban nasu zai koma gida da kuma a halin da zai dawo.

Sai dai wasu 'yan kasar na ganin ko da shugaban ya koma gida, ba shi da koshin lafiyar da zai yi cikakken jagoranci kasancewar ba wannan ne karon farko ba da Buharin ke fita neman magani.

Wannan dai shi ne karo na biyu da shugaba Buhari ke fita kasar waje neman magani sakamakon rashin lafiya.

Ko a watan Yunin 2016 ma sai da shugaban ya je Ingila kan ciwon kunne da ya yi fama da shi.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Tuna baya

Ko ma dai mene ne, masu sharhi na ganin Buhari ba zai bar baya da kura ba wajen jefa kasar cikin halin ni-'ya-su sakamakon gibin shugabanci kamar yadda ta faru a lokacin mulki tsohon shugaban kasa Umaru Musa 'Yar'adua.

A lokacin rashin lafiyar shugaba 'Yar'adua dai, an dade ana kai ruwa rana kafin a mika wa mataimakinsa, Goodluck Ebele Jonathan damar zama mukaddashin shugaban kasa.

Wannan ne kuma ya sanya al'amura suka tsaya cak a kasar, har zuwa lokacin da aka mika ragamar ga shugaba Goodluck Jonathan.

Yanzu haka dai masallatai da coci-cocin kasar sun dukufa wajen addu'ar nema wa shugaba Buhari lafiya.

Fiye da masallatan Juma'a 350, a jihar Borno suka yi masa addu'ar a ranar Juma'ar da ta gabata.

Labarai masu alaka

Karin bayani