An haramta bukukuwan Valentine a Pakistan

Pakistan valentine

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wasu kungiyoyin addinai suna gani Valentine na bata tarbiya

Wata kotu a Pakistan ta haramta bukukuwan ranar masoya ta Valentine a Islamabad, babban birnin kasar, tana mai cewa hakan ba dabi'ar Musulunci ba ce.

Babbar kotun birnin Islamabad ta bayar da umarnin hana duk wasu al'amura da suka shafi murnar ranar a wuraren taron jama'a, wanda zai fara aiki a ranar Litinin.

Ta kuma umarci kafafen yada labarai da cewa kada su yi duk wani labari da ya shafi ranar ta Valentine.

An bayar da umarnin ne sakamakon wani korafi da aka gabatar da ke cewa ranar Valentine ba ta dace da koyarwar Musulunci ba.

A shekarar da ta gabata ne shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain, ya bayyana ranar Valentine da cewa rana ce ta al'adun kasashen Yamma, wadda ba ta cikin al'adun kasar.