Mutane hudu sun mutu a wasan zamiyar kankara a Faransa

Faransa Hakkin mallakar hoto TOM FINNIGAN
Image caption Ma'aitatan ceto sun cigaba da bidar wadanda suka bace

Ma'aikatan ceto a kasar Faransa sun ce akalla mutane hudu sun mutu sakamakon dusar kankara a wasan zamiyar kankara a birnin Tignes, da ke kudu maso gabashin kasar.

An dai ce an binne rukunin 'yan wasan zamiyar kankarar tare da jagoransu bayan mutuwarsu sakamakon taho-mu-gama da wata dusar kankara wadda ta rushe a wurin da ba a bi.

Har yanzu, ba a san ainihin su wane ne mamatan ba, sai kuma rahotannin na cewa akwai matasa biyu masu shekara 18 da 15, a cikinsu.

Ana can kuma ana ci gaba da neman wasu karin masu wasan wadanda ake tsammanin kankarar ta binne su.

Labarai masu alaka