Manchester City ta zama ta biyu a tebirin Premier

Sergio Aguero Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Sergio Aguero ya zauna a benchi kafin ya maye gurbin Jesus

Manchester City ta zakuda zuwa mataki na biyu a saman tebirin gasar Premier ta Ingila bayan ta bi Bournemouth har gidan inda ta doke ta da ci 2-0.

Dan wasan City Sergio Aguero ya zauna a benchi tun da farko amma an sanya shi a wasa a minti na 14 inda ya maye gurbin Gabriel Jesus, wanda ya ji rauni.

Raheem Sterling ya soma zura kwallo, minti biyu bayan dan wasan Bournemouth Artur Boruc ya hana shi zura wata kwallon.

'Yan wasa na Bournemouth na ganin sun yi saurin mayar da martani, amma an ki amincewa da kwallon da Joshua King ya zura saboda ya rike rigar John Stones.

Golan City Willy Caballero ya kare kwallon da Harry Arter ya doka, kuma daga nan ne Tyrone Mings ya samu damar ci wa City kwallo ta biyu.

Labarai masu alaka