'Ku samar mana 'ya'ya da yawa a Ranar Valentine'

Valentine Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasashe irin su Pakistan da Indonesiya sun haramta bikin ranar Valentine

Gwamnatin mulkin soja ta Thailand tana amfani da Ranar Valentine domin karfafa wa mata gwiwa su haifi 'ya'ya da yawa, domin a cike gibin da rashin haihuwa ya haddasa a yawan al'ummar kasar.

Ma'aikatan gwamnati sun fito kan tituna a birnin Bangkok suna raba magungunan kara karfin mahaifa ga matasan mata.

Gwamnati ta ce wadannan magunguna suna aiki kwarai da gaske.

Thailand ta fara rufe gidajen karuwai

A shekarun 1970, ma'aurata a Thailand kan haifi 'ya'ya har shida, amma yanzu haihuwar ta ragu sosai.

An danganta hakan da sauyin rayuwa da rashin aure da wuri da kuma ci gaban da mata suka samu na ilimi da ke ba su damar zabar yadda rayuwarsu za ta kasance.

Ranar 14 ga watan Fabrairun kowace shekara dai ta kasance ranar nuna soyayya tsakanin ma'aurata ko kuma masu soyayya da juna.

Mutane kan mika kayututtuka kamar kudi ko katin soyayya ko kuma fure, ga wadanda suka kauna.

Wannan rana dai ta samo asali ne daga mabiya addinin Kirista, a inda suke karrama wani waliyyi mai suna Valentine da aka kashe a shekarar 269 bayan Yesu Almasihu.

Kasashen da dama sun rungumi wannan al'ada amma kuma babu wataa kasa da ta sanya ranar ta zamo ranar hutu.