'Mataimakin shugaban jami'a ya wawure N156m'

EFCC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar EFCC tana yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya EFCC, ta gurfanar da mataimakin shugaban jami'ar fasaha ta tarayya da ke Akure FUTA, a Kudancin kasar, inda ake tuhumarsa da laifuka tara da suka hada da yin sama da fadi da kudi sama da naira miliyan 156.

Tun a shekarar 2016 ne hukumar ta EFCC ta ce an aike mata da korafi kan zargin cin hanci da almundahana da wawure kudin jami'ar, da mataimakin shugabanta Farfesa Adebiyi G. Daramola da ma'ajinta Emmanuel Oresegun suka yi.

Daga cikin zargin da ake wa Farfesa Daramola har da batun cewa ya karbi alawus din gida bayan cewa yana zaune ne a gidan da gwamnati ta tanadar masa, da kuma alawus din kayan kawa na gida da yake karba duk shekara maimakon bayan shekara hudu-hudu da doka ta tanada.

A sanarwar da hukumar EFCC ta fitar, ta kuma ce mataimakin shugaban jami'ar ya ya yi ta amfani da kudin hukumar makaranta wajen gudanar da wasu abubuwa dsa suka shafe shi, da kuma biyan mambobin hukumar jami'ar wasu alawus-alawus ba bisa ka'ida ba.

Sai dai wadanda ake zargin sun musanta tuhumar da ake musu din.

Mai shari'a S. A. Bola, ya ba su beli kan sharadin naira miliyan 10 da kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya musu, wadanda dole su kasance Farfesoshi a jami'ar ta FUTA.

An dai dage shari'ar tasu zuwa watan Maris, amma za su ci gaba da kasancewa a hedikwatar hukumar tsaro ta farin kaya har sai sun cika sharuddan belin.

Labarai masu alaka