Mujallar Playboy ta yi nadamar cire hotunan batsa

Hoton wata mata a mujallar Playboy

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

Kamfanin Playboy ya tallata mujallar da zai fitar ta watan gobe a shafin Twitter

Mujallar Playboy ta sauya shawarar da ta yanke na daina saka hotunan batsa, inda ta ce ta yi kuskuren dakatar da wallafa hotunan batsar a shekarar da ta gabata.

Cooper Hefner wani babban jami'i ne na mujallar Playboy, wanda ya ce shawarar da ta yanke na janye hotunan batsa da take sakawa, "kuskure ne".

Ya kara da cewa, "Yau za mu koma kan abin da aka san mu da shi," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kamfanin Amurkan ya tallata mujallar da zai fitar a watan Maris da Afrilu da hoton jarumar da zai saka a mujallar, wadda aka bata take da maudu'in #NakedIsNormal, wato 'nuna tsiraici ba wani abu bane.'

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi maraba da sauya tunanin da Playboy ya yi, inda suka bayyana cewa, "Abu ne mai kyau" yayin da wasu kuma ke cewa mujalllar ta yanke shawarar ne saboda bata ciniki kamar yadda ta saba a baya.

Sai dai kuma da dama suna cewa mujallar ta gudu bata tsira ba saboda mutane na samun damar kallon batsa ba tare da sun biya kudi ba.

Mista Hefner ya ce, "Shi ne na farko da zai ce batsa da suke nunawa a mujallarsu ta zama tsohon yayi."

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Hugh Hefner ne ya samar da kamfanin Playboy a shekarar 1953

"Batsa bata taba zama matsalarmu ba saboda ba matsala ba ce, inji dan mai mujallar Playboy mai shekara 25.

Samir Husni, wani farfesa ne a jami'ar Mississippi, ya ce, "Dakatar da saka hotunan batsa ya sa masu karanta mujallar da dama sun ragu idan aka kwantanta da kasuwar da ta yi a baya."

Mujallar watan gobe zata kunshi wata kasida daga Scarlett Byrne, a kan kamfe din 'Free the Nipple' - wani kamfe da aka fara a Amurka a kan dokokin shayar da jarirai nono a bainar jama'a, da kuma matan da suke bude kirjinsu.

Amma kuma mujallar ta ce za ta soke bangaren da ke wallafa rubutu kan nishadantar da maza.

Cinikin da mujallar take yi ya matukar raguwa daga miliyan 5.6 a cikin shekarun 1970 zuwa kasa da 700,000 a bara.

Duk da haka, tambarin mujallar da ke nuna hoton zomo na daya daga cikin tamburan da aka sani a duniya sosai.