Fasinjoji za su fara amfani da Jirgi maras matuki a Dubai

Fasinja guda daya ne jirgin zai dauka

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Jirgin yana tafiyar kilomita 160 a sa'a daya

Wani jirgi maras matuki zai fara jigila a birnin Dubai daga watan Yuli, in ji Matt al-Tayer, babban jami'in kula da harkar sufuri na birnin.

Matt al-Tayer ya ce tuni jirgin, kirar ehang 184 wanda kasar China ta kera, ya yi shawagin gwaji.

Jirgin dai zai iya daukar fasinja guda daya da nauyinsa bai fice 100 kg ba kuma zai yi tafiyar da ba ta wuce ta minti 30 ba.

Fasinja na da zabi wajen yin amfani da na'urar sarrafa akalar jirgin mai amfani da yatsa domin zabar wurin da yake son jirgin ya kai shi.

Sai dai kuma jirgin ba shi da wasu na'urori a cikinsa kamar yadda jirgi ko kuma ababan hawa ke da su.

Jirgin dai yana da gudun da zai iya tafiyar kilomita 160 a awa daya a kasa sanna kuma zai iya amfani da batirin da aka caja sau daya, a wuri mai nisan kilomita 50.

"Hakika mun gwada wannan jirgi a sararin samaniyyar Dubai." in ji Matt al-Tayer.