Trump ya kwana biyu da sanin 'matsalolin' Flynn

Former White House national security adviser Michael Flynn. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Flynn's resignation raises questions about Mr Trump's relations with Russia, Republican lawmakers say

Wani mai magana da yawun fadar White House ya ce tun a makonnin da suka gabata ne Shugaba Donald Trump ya san cewa akwai matsala game da wayar da tsohon mai ba shi shawara a kan tsaro Michael Flynn ya yi da jakadan Rasha a Amurka.

Sean Spicer ya shaida wa manema labarai cewa shugaban ya yi ta "nazari da jujjuya batun a kowacce rana".

A baya dai, Mr Trump ya ce ba shi da masaniya kan rahotannin da ke cewa Mr Flynn ya yi wayar tarho da jakadan na Rasha a kasar.

Mr Spicer ya kara da cewa shugaban ya bukaci Mr Flynn ya ajiye aikinsa domin kada ci gaba da zamansa a kan mukamin ya haifar da zarge-zarge.

'Yan jam'iyyar Republican sun bi sahun takwarorinsu na sauran jam'iyyu wajen kiraye-kirayen a gudanar da bincike game da batun.

A taron manema labaran da ya yi ranar Talata, Mr Spicer ya yi karin haske kan dalilan da suka sanya Shugaba trump ya bukaci Mr Flynn ya ajiye mukaminsa, yana mai cewa "wannan batu ne da ya shafi gaskiya da rikon amana".

Mr Flynn ya sauka daga aiki ne bisa zargin da aka yi masa cewa ya tattauna da jakadan Rasha a Amurka kan yiwuwar cire wa Rasha wasu takunkumi tun ma kafin a rantsar da gwamnatin Trump, lamarin da ya keta dokokin kasar.

Da farko dai tsohon Janar din sojan na Amurka ya musanta cewa ya tattauna da Jakada Sergei Kislyak, kuma mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya fito bainar jama'a ya kare shi.

Amma daga bisani ya ce ya shirga karya a kan batun.

Laftanar Janar Keith Kellogg (mai ritaya) ne ya maye gurbin Mr Flynn.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An dauki hoton Mr Flynn yana cin abincin dare tare da Shugaban Rasha Vladimir Putin a watan Disambar 2015
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Laftanar Janar Keith Kellogg yana da kwarewa ta sama da shekara 30 a rundunar sojin Amurka

Labarai masu alaka