Paris St-Germain ta lallasa Barcelona da ci 4-0

Angel Di Maria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon dan wasan Manchester United Angel di Maria ya zura kwalonsa ta takwas a kakar wasa ta bana.

Angel di Maria ya haskaka sosai bayan ya zura kwallaye biyu a wasan da Paris St-Germain ta wulakanta Barcelona da ci 4-0, abin da ke yin barazana ga yiwuwar Barca ta kai wa zagayen dab da na kusa da karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai a karon farko cikin shekara goma.

'Yan wasan PSG sun mamaye wasan, sannan suka wuce gaban Barca ta hanyar kwallon da Di Maria ya zura daga bugun tazara.

Julian Draxler ne ya zura kwallo ta biyu kafin Di Maria ya kara kwallonsa ta biyu.

Edinson Cavani ya zura kwallon karshe.

Barcelona dai ba ta yi wani kuzari ba- inda 'yan wasa irin su Lionel Messi, Luis Suarez da kuma Neymar suka kasance tamkar ba sa cikin filin - kuma ba su yi wani yunkurin a-zo-a-gani ba sai saura minti bakwai kafin a kammala wasan lokacin da Samuel Umtiti ya doka kwallo da ka a kusa da ragar PSG.

Yanzu dai Barca na cikin tsaka-mai-wuya domin kuwa ba karamin kokari za ta yi ba idan tana son ci gaba da zama a cikin gasar.

Za su karbi bakuncin PSG ranar 8 ga watan Maris.

A tarihin gasar Zakarun Turai ba a taba samun kungiyar da ta cike gibin da aka ba ta na kwallaye hudu ba.

Messi ba shi da katabus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Messi ya gaza yin katabus

Barcelona ta kai matakin sili-ɗaya-kwale ne bayan da ta yi nasara a rukunin C, inda ta ci biyar cikin shida na wasanin da ta yi.

Wasa daya da ta sha kaye a cikinsa shi ne Manchester City ta doke su da ci 3-1.

A wasan, sun yi kokari sun ci kwallo daya - wadda Messi ya zura.

Sau da dama dai 'yan wasan Barca kan kasance cike da kuzari, amma a wannan karon kamar ruwa ya doke su.

A wannan karon Messi, wanda ke da ilhamar zura kwallo ko kuma bai wa wani ya zura kwallon, ya tafka kura-kurai da dama.

Wannan karawa ita ce daya daga cikin wasanni mafi muni da Barcelona ta yi a tarihinta, ko da yake 'yan wasan PSG na cike da kuzari da shauki, kuma a gaskiya ma, ya kamata a ce sun ci kwallaye fiye da hudu.

Sun kai hari 16, 10 daga ciki masu hatsarin gaske.