Nigeria: Kotu ta mallaka wa gwamnati dalolin Andrew Yakubu

Hakkin mallakar hoto Encyclopedia
Image caption Andrew Yakubu ya rike matsayin shugaban NNPC daga shekarar 2014 zuwa 2014

Wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zamanta a jihar Kano ta mallaka wa gwamnatin Najeriya naira biliyan uku da aka gano a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na kasar, NNPC.

Hakan ya biyo bayan bukatar da hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC, ta shigar a gaban kotun.

A ranar Talata ne kotun ta bayar da umarnin cewa kudin da suka kai kusan $10 da kuma fam 750,000 da aka gano a gidan Mista Yakubu da ke Kaduna sun zama na gwamnatin Najeriyar.

An gano sabuwar almundahana a NNPC

Nigeria: 'Dole NNPC ya biya gwamnati kudi'

Umarnin kotu

Kotun wadda mai shari'a Zainab Abubakar ke jagoranta, ta bayar da wannan umarni ne a matsayin na wucin gadi har sai lokacin da aka kammala shari'a a kan batun kudaden.

Ko da yake ya zuwa yanzu ba a kai ga gurfanar da Mista Yakuba ba tukuna a gaban kotu a kan batun kudaden da aka samu a gidan nasa.

Sai dai kawo yanzu tsohon shugan na NNPC na tsare a hannun hukmar ta EFCC wanda ke ci gaba da bincike a kansa.

A makon da ya gabata ne shugaban riko na hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu, ya shaida wa majalisar wakilan kasar cewa sun samu kusan dala miliyan 10 da kuma fam 750,000 a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC, Mista Andrew Yakubu, a yayin da suka kai wani samame.

An kiyasata yawan kudin a matsayin naira biliyan uku.

Labarai masu alaka