Wa ke son zama tauraron dan jarida kamar Komla Dumor?

Komla Dumor
Image caption BBC tana neman matashi mai basira wanda zai gaji Komla

Kafar yada labarai ta BBC tana neman tauraron dan jarida a Afirka da zai lashe gasar karrama tsohon ma'aikacinta Komla Dumor.

Wannan ne karo na uku da ake gudanar da gasar.

Ana gayyatar 'yan jarida daga nahiyar Afirka da su shiga wannan gasa, wadda ke son zakulo tare da bayar da dama ga mutane masu dumbin basira a nahiyar.

Wanda ya lashe kyautar zai samu damar kara kwarewa da gogewa a kan aikin jarida, tare da ma'aikatan BBC a London na tsawon watanni uku.

Za a rufe shiga gasar ranar 15 ga watan Maris da misalin karfe 11.59 na dare agogon GMT.

An fara shirya gasar ne domin tunawa da hazikin dan jaridar nan dan asalin kasar Ghana Komla Dumor, wanda kuma yake gabatar da labaran duniya a BBC, wanda ya mutu a shekarar 2014, yana dan shekara 41.

Komla hazikin dan jarida ne wanda bai yi tsawon rai ba, amma kuma ya taka rawa a Ghana da Afrika da kuma duniya baki daya a gidan rediyon Joy FM da kuma BBC.

Saboda lakantar aikin jarida, ya iya gabatar da labaran duniya na BBC baki daya.

BBC ta shirya wannan kyauta ce domin ci gaba da tunawa da Komla.

Wa ye zai iya shiga gasar?

Domin s

Duk wani dan Afrika da yake zama kuma yake aiki a nahiyar, wanda kuma ya lakanci aikin jarida yake da basirar bayar da labaran da suka shafi Afrika da kuma burin zama tauraron dan jarida a nan gaba.

Wata mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Kenya Nancy Kacungira, ce ta lashe kyautar a shekarar 2015.

A shekarar 2016 kuma Didi Akinyelure wata 'yan jarida a Najeriya ce ta lashe kyautar.

Image caption Ms Akinyelure ta ce ta samu tarin ilimin kwarewa a aikin jarida a BBC

A lokacin da ta yi aiki da BBC Ms Akinyelure ta samu damar zuwa kasar Ivory Coast inda ta yi bincike kan sabbin damarmaki na yin cakulat a kananan masana'antu.

"Aikin da na yi da BBC ya sauya rayuwata sosai," inji Ms Akinyelure.

Ta kara da cewa, "Gaskiya ina shawartar mutane su yi amfani da wannan damar sosai su shiga gasar nan."

Daraktar kafar yada labarai ta BBC Francesca Unsworth, ta ce a shirye BBC take ta ci gaba da gudanar da wannan gasa don karfafa wa 'yan jarida gwiwa.

Labarai masu alaka