Mutumin da ya ci mutuncin musulmi na takara a Indonesia

Indonesia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Al'umman Indonesia miliyan goma na jefa kuri'a

Al'ummar babban birnin kasar Indonesia, Jakarta, suna zaben sabon Gwamna, a dai-dai a lokacin da ake zargin gwamnan jihar mai ci, Basuki Tjahaja Purnama da aikata sabo.

Ana zargin Mista Purnama da zagin Musulunci, bayan da ya zargi abokin adawarsa da yin amfani da Kur'ani yana yaudarar masu jefa kuri'a.

Sai dai gwamnan ya ki amince wa da zargin, a inda ya ce ba da muslmai yake ba, illa dai yana yi wa 'yan siyasa shagube ne.

Basuki Tjahaja Purnama, ko kuma "Ahok", shi ne farkon kirista daga kabilar Sin da aka zaba a matsayin gwamna a tsawon shekaru 50 kuma yanzu haka yana takarar neman yin tazarce.

Dubbun miliyoyin 'yan Indonesia sun jefa kuri'a a yankin.

Wannan zaben na zuwa ne a dai-dai lokacin da mista Purnama yake fuskantar shari'a kan kalaman batancin da ake tuhumar sa da yi.

A watan Disambar 2016 ne dai aka fara sauraron shari'ar, kuma idan har an same shi da laifi to zai yi zaman gidan kaso na shekara biyar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana zanga-zanga a babban birnin Indonesia da Gwamnan

Kidaya da aka yi bayan kare zaben ta nuna cewa Mista Purnama na gaba da tsohon ministan kula da harkokin Ilimi, Anies Baswedan.

Sai dai kuma ya samu kasa da kashi 50 cikin dari da yake bukata domin lashe zabe.

Bisa dokar kasar dai mutumin da zai ci zaben sai ya samu kaso 50 na kuri'ar da aka kada ko kuma a je zagaye na biyu a watan Afrilu.

Za a bayyana sakamakon zaben a karshen watan Fabrairu.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Za a bayyana sakamakon zaben karshen wata mai kuwa