Mene ne dalilin da ya sa tsutsa ta auka wa Afirka?

Tsutsa na addabar gonakin Afirka

Asalin hoton, CABI

Bayanan hoto,

Tsutsa na addabar gonakin Afirka

Masana kimiyya na gargaɗin cewa yankunan kudancin Afirka waɗanda da ma tuni suke fama da fari a yanzu suna fuskantar wata gagarumar matsalar abinci saboda mamayar wata tsutsa mai laƙume amfanin gona wadda a turance ake kira "fall armyworm".

Ƙwararru a faɗin duniya suna ganawa a Harare babban birnin ƙasar Zimbabwe don ɓullo da wani tsari na yaƙi da wannan tsutsa.

Wace irin tsutsa ce wannan?

Sunanta na armyworms yana ɗan karkatar da hankali. Ba wai tsutsa ba ce kamar yadda aka sani, wani mayunwacin ƙwaro da aka ƙyanƙyashe shi da sigar tsutsa kuma yake cinye amfanin gona kafin balagarsa.

Sabuwar tsutsa ce, ba kamar wadda muka sani a nahiyar Afirka ba tsawon shekaru.

Daga ina ta zo?

Asalinta daga nahiyar Amurka, sai dai ƙwararru ba su da tabbaci kan yadda ta yi ta shigo Afirka.

Wani ra'ayi na cewa ƙwayayenta ne ko ma ita kanta da kanta ta laɓe cikin wasu amfanin gona da ake shigowa da su, ko kuma ta biyo jirgin sama ne ma ta shigo.

Me ya sa ta kasance barazana ga noma?

  • Tana da yunwa ainun (kuma ba ta zaɓi) - Wannan tsutsa ta fi son cin tsabar masara da sauran hatsi, kamar takwararta ta Afirka, amma ita tana kuma far wa auduga da waken suya da dankalin turawa da tsiron taba. Idan ta danno, takan lalata uku cikin huɗu na amfanin gona.
  • Abokiyar ƙiyayya ce da ba a san ta ba - Gwamnatoci da yankuna da manoma ba su taɓa wata alaƙa da wannan tsutsa ba, wadda ka iya zama mai wuyar sha'ani idan an kwatanta da takwararta wadda aka sani a Afirka.
Bayanan hoto,

Tsutsar tana iya lalata daukacin gona

  • Tana da sauri - A cewar Hukumar abinci da aikin gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya, a cikin mako shida kacal tsutsar ta fantsama cikin ƙasa shida a kudancin Afirka.
  • Tana tafiya da nisa kuma tana bazuwa - Tsutsar ita ce mai lalata amfanin gona amma "balagaggen ƙwaronta ne yake yin ƙaura mai nisa kuma ta haka ta iya shigo wa Afirka," a cewar Farfesa Ken Wilson, wani ƙwararre kan sha'anin tsutsa.
  • Ba kawai tsoffin amfanin gona take far wa ba - Masara ita ce abincin kowa a yankuna da dama da aka shaida tsutsar.
  • Tana da wuyar sha'ani - Tsutsar tana laɓewa ne a cikin karan masara ta yadda manomi ba zai iya farga da ita da wuri ba.
  • Bahagon lokaci - Ta zo ne bayan fari na tsawon shekara biyu, wanda tuni ya shafi mutane sama da miliyan 40 a yankin, inda ya janyo ƙarancin abinci da kashi 15 cikin 100 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A ina take?

Afirka ta kudu da Zimbabwe da Malawi da Zambia da Namibia da kuma Mozambique su ne manyan ƙasashen da ake jin tsutsar ta bazu cikinsu a cewar Hukumar abinci da aikin gona ta duniya.

Ta ce a watan Janairun 2016 ne aka fara ba da rahoton ɓullar tsutsar a tsibirin Sao Tome da Principe.

Chimenya Phiri, Manomi a Malawi:

Bayanan hoto,

Tsutsar ta kuma auka wa gonakin ƙasar Malawi

"Waɗannan tsutsotsi sun auka wa ganyayyakin masara,da furenta kuma saboda suna shiga can cikin karan tsirrai, yana da wuya ka kula.Sai ka matsa kusa sosai ne za ka iya gane cewa ai duk sun cinye tsiron amfani"

Sauran masu bincike sun ba da rahoton ɓullarta a yankunan Afirka ta yamma, ciki har da Nijeriya da Ghana.

Sai dai gwamnatocin Zimbabwe da Afirka ta kudu ne kawai suka fito fili suka tabbatar cewa suna da matsala taƙamaimai da wannan tsutsa.

Wace irin ɓarna ya zuwa yanzu suka yi?

Babu masaniya taƙamaimai, saboda ƙasashe da dama da abin ya shafa ba su bayar da bayanai ba ya zuwa yanzu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce gano adadin kadadar da tsutsar ta shafa da kuma tsananin ɓarnarta na daga cikin manyan manufofin taron ƙolin gaggawa da ake yi a Zimbabwe.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Afirka ta kudu wadda ita ma tsutsar ta shafi gonakinta, ita ce ƙasa mafi noman masara a yankin

Afirka ta kudu, ƙasa mafi samar da masara a yankinsu, ta tabbatar da ɓarnar da tsutsar ta yi wa amfanin gona a lardi guda shida na ƙasar.

Gwamnatin Zambia ta ce kadada dubu 130 tsutsar ta shafa a faɗin ƙasar.

Me za a iya yi a dakatar da ita?

Ana iya amfani da maganin kashe ƙwari da sinadarai don kawar da tsutsar a farkon rayuwarta, amma idan ba haka ba zai yi wuyar gaske a iya magance ta, wani nau'in tsutsar yana bijirewa magani a cewar ƙwararru.

Bayanan hoto,

Masana kimiyya na fatan ganin an haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunkarar wannan mamaya

Sauran wasu dabarun sun ƙunshi amfani da tsuntsaye da za su cinye su ko kuma ƙona sashen gonar da suka cinye amfaninsa, in ji David Phiri, babban jami'i a hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Afirka ta kudu.

Zambia, inda ake jin na ɗaya cikin ƙasashen da annobar ta ɓarke, sun yi amfani da jiragen soja wajen yin feshi, lamarin da ya sa wasu amfanin gonar suka iya farfaɗowa kamar yadda wani jami'in hukumar taƙaita annoba ta ƙasar ya faɗa wa BBC.

Sai me kuma?

Gargaɗin hukumar abinci da aikin gona ta duniya ba labari ne mai daɗi ba, don kuwa ya nuna cewa al'amura ka iya yin muni kafin a iya shawo kansu.

"Gobara ce daga kogi - kamata ya yi hatta ƙasashen da a yanzu tsutsar ba ta ɓulla ba, su shirya," in ji Mr Phiri.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A shekara ta 2015 ne ƙasar Botswana ta fuskanci fari mafi muni cikin shekara 30

Cibiyoyin binciken kimiyya sun kuma ankaras, inda suka bayyana tsutsar a matsayin wata babbar barazana ga wadata ƙasashe da abinci da kuma cinikin amfanin gona a Afirka.

Mr Phiri ya ce duk da haka idan ƙasashe a faɗin nahiyar za su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunkarar annobar, to ba shakka ana iya samun waraka.

"Ba za mu iya kakkaɓe ta ba, amma muna iya gano hanyoyin taƙaita yaɗuwarta," in ji Phiri.