Yadda aka kashe 'yan jarida a Jamhuriyyar Dominica

Dan sanda jamhuriyar Dominica a lokacin da yake gadin gidan rediyo FM.103

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

'Yan sandan jamhuriyyar Dominca sun fara bincike domin gano wadanda suka kai wanna

An kama wasu maza biyu bayan bisa zargin kisan wasu 'yan jarida biyu, a lokacin da suke gabatar da shiri kai tsaye a jamhuriyyar Dominica.

Daya daga cikin 'yan jaridar na daukar hoton bidiyon wani shiri a shafin Facebook, a lokacin da aka harbe shi.

Karar bidinga ce ta dauke hankalin mai daukar hoton bidiyon, sai kuma wata mata da ta gigice take ta ihun fadin harbi! harbi!! harbi!!!.

'Yan sanda sun ce, a ranar Talata ne aka yi harbin a garin San Pedro de Macoris da ke gabashin Santo Domingo, babban birnin kasar.

Luis Manuel Medina mai gabatar da shiri da Leo Martinez mai hada shiri ne 'yan jaridar da aka kashe.

Ba a gurfanar da mutanen biyu, wadanda ake zargi a gaban kotu ba kuma 'yan sanda sun ce ba su san dalilin da ya sa suka aikata haka ba.

Antoni janar Jean Rodriguez ya ce " an fara bincike kuma zamu yi iya kokarinmu da karfin ikon da muke da shi domin gano gaskiya".

A watan Augustan 2015 ma an kashe wasu 'yan jarida biyu, a lokacin da suke gabatar da shirin talabijin kai tsaye a Virginia.