An sa dokar ta baci kan gurbatar yanayi a Fatakwal

Hannun wani mazaunin Port Harcourt

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hayaki ya kan turnuke birnin inda yake hana mutane jin dadin yanayin

Ma'aikatar kula da muhalli ta Najeriya ta ce an kaddamar da dokar ta baci kan gurbatar yanayi a jihar Fatakwal babban birnin jihar da ke Arewacin kasar.

A wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta kuma ce na rufe kamfanin mai na Asphalt saboda yadda yake tuttudar hayaki mai guba da ke cutar da al'umma.

A ranar Talata ne dai mazauna birnin suka yi zanga-zanga inda suka rika daga hannayensu sama don nuna yadda suka baci da tokar hayaki.

Charles Adolor, wani dan kasuwa mazaunin birnin ya ce shi da matarsa sai sun saka kyalle sun rufe fuskarsu daga shakar hayakin domin kare lafiyarsu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce a watan Nuwamba ne dai hayakin ya fara turnuke birnin, kuma a karshe jami'ai suka kawo kwararru a makon da ya gabata domin yin bincike kan lamarin.

Dama dai ana yawan samun matsalar gurbatar yanayi ko muhalli a Najeriya musamman a yankin Kudu maso Kudancin kasar.

A shekarar da ta gabata ma gidauniyar kula da muhalli ta Jamus a Najeriya, HBS, ta ce ƙasashe da dama a nahiyar Afirka sun yi wa Najeriyar fintinkau wajen rungumar makamashi maras gurbata Muhalli.