An sace keken wani minista a Belgium

Hoton wurin da minstan ya kulle kekensa da aka sace Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Hoton wurin da minstan ya kulle kekensa da aka sace

An sace keken wani ministan kasar Belgium bayan ya tuka shi zuwa wajen bikin sanar da matakin gwamnati na zuba jari kan gina sabbin titunan keke.

Mai magana da yawun ministan ya ce an sace keken ministan sufuri, Ben Weyts ne duk da cewa ya kulle shi a kusa da wata tashar layin dogo da ke kudancin Brussels.

Sa'a daya bayan an kammala taron ne ministan ya dawo inda ya kulle keken amma ya ga wurin fayau.

Kakakin ministan ya kara da cewa daga nan ne Mr Weyts ya buga wa direbansa wayar tarho domin ya je ya dauke shi.

Ministan na fatan cewa na'urar daukar hoto ta tsaro da aka maƙala a yankin za ta taimaka wa 'yan sanda wajen gano ɓarawon keken.

'Yan sanda sun sha alwashin tsaurara tsaro a yankin.

A wajen taron manema labaran da ministan ya halarta kan zuba jari a titunan keke kuwa, Mr Weyts ya ce za a kashe $316m domin gina titunan keke nan da shekarar 2019, a wani shiri na bunkasa sufuri.

Labarai masu alaka