Indiya za ta kafa dokar hana auren facaka

Indian costly marriage Hakkin mallakar hoto JANARDHANA REDDY FAMILY
Image caption Attajiri Janardhana da 'yarsa tare da sauran dangi a bikin aurenta da aka iyasta an kashe rupee biliyan biyar

Indiya na shirin ɓullo da wata sabuwar da za ta rage kashe-kashen kuɗi na babu gaira babu dalili a shagulgulan aure a faɗin ƙasar.

ƙudurin dokar ba kawai taƙaita yawan mahalarta da ire-iren abincin da za a ci a bikin aure zai yi ba don rage almubazzaranci, zai sanya wani "haraji" a kan auren nuna ƙasaita da aka kashe maƙudan kuɗi a cikinsa.

Ma'auratan da suka kashe kuɗi sama da rupee dubu 500 kimanin Naira miliyan huɗu za su bayar da kashi 10 cikin 100 na kuɗin ga wasu amare matalauta don taimaka musu wajen biyan dukiyar aurensu.

Matakin ya zo ne sakamakon ƙaruwar nuna ɓacin rai kan maƙudan kuɗin da wasu ke fallasarwa a yayin aure.

A watan Nuwamba, bikin auren wani ɗan kasuwa da 'yar wata tsohuwar ministar jiha na tsawon kwana biyar, ya laƙume kimanin rupee biliyan biyar, lamarin da ya janyo tada jijiyoyin wuya, a daidai lokacin da miliyoyin Indiyawa ke fama da matsalar ƙarancin kuɗi.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A wani ɓangaren Indiya, mutane na shafe tsawon lokaci a kan layi don canza takardun kuɗinsu waɗanda gwamnatin ƙasar ke shirin sauyawa

Daga cikin almubazzarancin da aka yi yayin bikin, akwai katunan gayyata masu ruwan gwal da aka yi su da fuskar talbijin a kan kuɗi rupee miliyan 10.

'Yar majalisa Ranjeet Ranjan wadda ke gabatar da ƙudurin dokar tilasta rijistar aure da hana almubazzaranci na shekara ta 2016 ta faɗa wa kamfanin dillancin labaran Indiya PTI cewa auratayya ta koma "kawai wata dama ta nuna isa da fariya" amma ba matsayinta na tubalin gina al'umma ba.

"Don haka, masu ƙaramin ƙarfi na fuskantar gagarumin matsin lamba a kan su kashe ƙarin kuɗaɗe" ta ce "Akwai buƙatar a taka wa hakan burki don kuwa ba shi da wata fa'ida ga al'umma."

Kaɗan daga cikin bukukuwan aure mafi tsada a duniya:

  • Vanisha Mittal, 'yar attijiri na biyu mafi tarin dukiya a Indiya, Lakshmi Mittal ta auri wani Amit Bhatia a wani shagali da aka ce wai an kashe dala miliyan 74 a shekara ta 2004. A cewar mujallar Forbes, dangin amaryar sun yi jigilar baƙi dubu 1 zuwa Faransa a jirgin sama don gudanar da shagulgula.
  • Ana jin auren Yarima Charles da Diana, Gimbiyar Wales a 1981 ya kai kimanin fam miliyan 30 - a yanzu kuɗin ya kai kwatankwacin fam miliyan 116. Idan an kwatanta da auren ɗansu William da Kate Middleton a kan fam miliyan 20 a cewar jaridar Daily Mail.
  • A watan Maris, ɗan gidan hamshaƙin attijirin ƙasar Rasha, Said Gutseriev ya auri Khadija Uzhakhovs a Moscow. Ana jin cewa an kashe sama da dala miliyan 1 da dubu 200 kan tufafin fitar auren amarya kuma a cewar MailOnline, baƙin da aka gayyata sun raƙashe ta hanyar raye-raye da waƙe-waƙe ba kawai daga mashahurin mawaƙi guda daya ba, fitattun mawaƙa uku: Jennifer Lopez da Sting da Enrique Iglesias. Yawan kuɗin da aka kashe? Mai yiwuwa dala biliyan ɗaya.

Labarai masu alaka