Bayern Munich ta lallasa Arsenal da ci 5-1

Alexis Sanchez

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Alexis Sanchez ya zura kwallonsa ta 20 a kakar wasa ta bana

Fatan Arsenal na daukar kofin Zakarun Turai ya dusashe bayan Bayern Munich ta doke ta da ci 5-1.

'Yan kungiyar ta Arsenal, wadanda aka murkushe a matakin farko na gasar a kakar wasanni shida a baya, kuma wadda sau Bayern na kawar da ita, ta yi asarar kwallo biyar da kuma 75 na rike kwallo a Jamus.

Daga baya dai Arsenal ta dan yi tagomashi inda Alexis Sanchez ya zura kwallo.

Sai dai bayan dan wasan Arsenal Laurent Koscielny ya yi rauni bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Bayern ta yunkura sosai inda Robert Lewandowski ya zura tasa kwallon kana Thiago Alcantara ya zura kwallaye biyu.

Daga bisani kuma Thomas Muller, wanda ya shiga wasan daga baya, ya zura kwallo ta biyar.

Hakan dai ya bar Arsenal cikin matukar rudanin da da wuya ta warware daga gare shi.