Shin Buhari yana gida ne ko yana asibiti?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shin Buhari yana gida ne ko yana asibiti?

Kusan makonni hudu kenan rabon da a ga shugaba Buhari na Najeriya a bainar jama'a ko a kafafen yada labarai, tun lokacin da ya ce ya tafi hutu Birtaniya.

Masu magana da yawunsa sun ce ya tsawaita hutun nasa saboda yana jiran sakamakon gwaje-gwajen asibiti da aka yi masa, sai dai ba su bayar da tabbacin ranar dawowarsa ba.

'Yan Najeriya dai suna ta tofa tasu kan wannan batu, inda wasu ke cewa lallai jikin nasa ne ya yi tsanani har ma ake yada jita-jitar mutuwarsa, yayin da wasu kuwa ke cewa ba tsanani jikin ya yi ba, sun yarda da cewa sakamakon yake jira.

Hakan ne ya sa BBC ta jiyo ra'ayoyin wasu 'yan kasar kan wannan lamari.

Labarai masu alaka