Abin da sojin Nigeria ke yi 'da ba ku sani ba'
Baya ga yaki da kungiyar Boko Haram da sojojin Najeriya ke yi, suna kuma yin ayyukan agaji da suka hada da taimakon wadanda yaki ya galabaitar da rayuwarsu.

A ziyarar da tawagar BBC ta kai jihar Borno, ta ga wata cibiyar lafiya da rundunar sojin sama ta Najeriya ta gina a sansanin 'yan gudun hijira na Dalori, inda sojojin ke taimakawa marasa lafiya.
Kuma dukkan ma'aikatan wannan cibiya sojoji ne, wadanda suke da kwarewa a kan harkar lafiya. Suna kuma aikin taimakon jama'a ba dare ba rana.
A wannan cibiya ta lafiya dai ana duba marasa lafiya maza da mata da yara, ana kuma kwantar da marasa lafiyar da ke bukatar a duba su sosai.
Wani abin da ake yi kuma a cibiyar shi ne har haihuwa mata suna yi, "Kuma suna samun kular da suke bukata da su da jariransu." inji sojojin da ke kula da wajen.
"Wannan dakin gwaje-gwaje ne da ke cibiyar, inda ake gwajin jini da fitsari da sauransu don gano abin da ke damun marasa lafiya," inji tawagar BBC.
Mafi yawan marasa lafiyar mata ne da yara wadanda suka yi matukar shan wahala sakamakon halin da suka tsinci kansu saboda rikicin Boko Haram.
Baya ga cibiyar lafiya ta sansanin 'yan gudun hijira na Dalori, sojojin sun kuma bude wata cibiyar lafiyar a garin Bama, inda nan ma suke aikin taimakon jama'a.
An dai sha zargin sojojin Najeriya da cin zarafin bil adama da kuma take hakkokinsu, musamman a yakin da suke yi da Boko Haram.
Sai dai ana ganin irin wannan aikin taimako da suke yi zai zama sila ta dinke barakar da ke tsakanin sojojin da al'ummar yankin.
Baya ga gina cibiyoyin lafiya kuma, sojojin sun gina rijiyoyin burtsatsai domin tallafawa mazauna sansanonin 'yan gudun hijirar.