A bai wa Nigeria kudin Diezani — Kotu

Diezani
Image caption Misis Madueke ta kasance ta hannun damar tsohon shugaba Goodluck Jonathan

Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince a halatta tare da mallakawa gwamnatin kasar kudaden da aka samu daga wajen tsohuwar ministar mai, Diezani Allison-Madueke.

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta annati ta EFCC ce ta bukaci kotun ta mallakawa gwamnati kudin da yawansu ya kai sama da dala miliyan 150.

Dama dai kafin yanzu kotun ta damkawa gwamnati kudin su zauna a hannunta kafin a kammala shari'a.

Amma wannan hukuncin na nuna cewa kudin ya zama na gwamnati dundundun.

Wannan hukunci na nuna cewa kudin ba na halal din Misis Madueke ba ne, bisa binciken da aka gudanar.

Tun a watan Janairun wannan shekarar ne, tsohuwar Ministar ta mika wa gwamnatin kasar dalar Amurka miliyan 153 da ake zargin ta sata daga asusun gwamnati a lokacin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Nigeria: Tsohuwar ministar mai ta mika dala miliyan 153 ga EFCC

EFCC ta kwace gwala-gwalan N593m na Diezani

Hakan ya biyo bayan wani hukunci da wata kotu ta yanke a birnin Legas na tilasta matar mika kudaden ga gwamnatin har a tabbatar da halaccinsu ko akasin haka.

Labarai masu alaka