Harin sama ya kashe 'yan zaman makoki a Yemen

Yemen
Image caption An sha kai hare-hare gidan makoki bisa kuskure a Yemen

Rahotanni na cewa an kashe mata takwas da wani yaro, a wani hari da aka kai ta sama a lokacin da ake zaman makoki a wani gida kusa da Sanaa babban birnin Yemen.

Majiyoyin lafiya sun ce a kalla wasu matan fiye da 10 sun samu raunuka sakamakon harin.

Kakakin 'yan tawayen Houthi ya ce harin ya biyo bayan wani ne da aka kai wa masu aikin bayar da agajin gaggawa a Arhab, mai nisan kilomita 25 daga Sanaa.

'Yan tawayen na zargin kasar Amurka da gamayyar kawancen Saudiyya da jawo zub da jini, amma har yanzu kasashen basu mayar da martani ba.

Gamayyar kawancen da Saudiyya ke jagoranta suna yakar 'yan Houthis da kuma sojoji masu mara wa tsohon shugaban kasar Yemen, Ali Abdullah Saleh baya, tun watan Maris na shekarar 2015.

Manufar ita ce, su sake kawo gwamnatin Abdrabbuh Mansour Hadi kan mulki wanda duk kasashen duniya suka amince da shi a matsayin shugaban kasa.

An kai hari kan masu jana'iza a Yemen ne bisa kuskure— Saudiya

Kun san hare-haren da soji suka kai bisa kuskure?

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dubban mutane na fuskantar karancin abinci da ruwa

Yakin da ya ki ci ya ki chanyewa a kasar Yemen ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula fiye da 10,000 da kuma sa mutane fiye da miliyan uku gudun hijira, tun shekara 2015.

Kungiyar Likitoci ta Medicines and Fronters ta yi gargadi cewa a wannan makon abubuwa zasu kara rikicewa a birnin Taiz, inda ake ci gaba da kai hare-hare kan asibitoci kuma mutane 200,000 na fuskantar karancin abinci da ruwa da magunguna.

An soki kasar Amurka a watan da ya gabata a kan harin da ta kai wani kauye a tsakiyar kasar Yemen, inda fararen hala da dama suka mutu yawancin su kuma yara.

Sun kai harin ne, a gidan da suke tsamnani na shugaban al-Qaeda ne.

Labarai masu alaka