Gudanar da zabe ya mana tsada a bana —DR Congo

Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Joseph Kabila da rashin son sauka daga mulki

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Tarayyar Afirka sun bayyana damuwarsu a kan yadda ba a samun ci gaba a harkokin siyasar Jamhuriyyar Demokradiyar Congo.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da ministan kasafin kudin kasar, Pierre Kangudia ya fitar da ke cewa gwamnati ba ta da kudin da za ta iya gudanar da zaben shugaban kasa, wanda yawan su ya kai dala biliyan 1.8.

A shekarar da ta gabata ne gwamnati da 'yan adawa suka amince cewa za a gudanar zaben a karshen shekarar 2017.

Lokacin da aka zaba na jefa kuri'a ya dace da wata yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu domin kawo karshen rikicin siyasa da kasar ke fama da shi.

Wa'adin Shugaba Joseph Kabila ya zo karshe a watan Nuwanbar 2016, inda 'yan adawa ke zarginsa da jinkirta zaben domin ya ci gaba da mulkin kasar.

Labarai masu alaka