Kungiyar Boko Haram ta kai hari kan jirgin sojin Nigeria

Daya daga cikin jiragen saman yaki na Najeriya Hakkin mallakar hoto NAF
Image caption Rudunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kawar da maharan

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce wasu 'yan Boko Haram sun kai wa wani jirginta mai saukar ungulu hari a lokacin da yake kai ma'aikatan lafiya garin Gwoza na Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da kakakinta, Guruf Kyaftin Ayodele Famuyiwa, ya sanya wa hannu, ta ce 'yan Boko Haram din sun yi harbe-harbe a kan jirgin kirar Mi-17, amma ba wanda ya rasa ransa sai dai matukin jirgin ya yi rauni.

Jirgin dai ya tashi ne daga Maiduguri don kai ma'aikatan wadanda ke gudanar da wani shiri na kwanaki biyu na taimaka wa marasa lafiya a garin na Gwoza.

Sanarwar ta kara da cewa duk da raunin da ya yi, matukin jirgin ya kai ma'aikatan inda ya nufa domin ganin shirin ya ci gaba ba tare da wani tsaiko ba.

Bayan harin, a cewar rundunar, an tashi wani jirgin saman yaki da kuma wani jirgin mai saukar ungulu dauke da manyan bidigogi zuwa yankin, wanda ke tsakanin Bama da Gwoza domin kawar da maharan.

Ta kuma ce rahotannin sirri daga dakarun sojin ƙasa sun tabbatar cewa an kashe 'yan Boko Haram din, lamarin da ke nuna cewa an yi nasara a harin da aka kai.

Ba wannan ba ne dai karo na farko da Boko Haram ke yi wa sojojin Najeriya kwanton bauna, duk kuwa da ikirarin da hukumomi ke yi cewa an karya lagon mayakan kungiyar.

Labarai masu alaka

Karin bayani