Sinadarin Vitamin D na iya ceto mutane daga mura

Kwayar sinadrin vitamin D

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Garkuwar jiki na amfani da sinadarin Vitamnin D wajen samar da halittar da ke kashe kwayoyin cuta

Sinadarin vitamin D da ake samu daga hasken rana yana da muhammanci ga lafiyar kasusuwan mutum, amma kuma yana da amfani wajen inganta garkuwar jiki.

A wani sharhi da aka wallafa a mujallar lafiya ta Birtaniya, ya ce ya kamata a rika cin abinci mai dauke da sinadarin Vitamin D.

Garkuwar jiki na amfani da sinadarin Vitamnin D wajen samar da halittar da ke kashe kwayoyin cuta da ke haddasa rami a kwayoyin cututtuka na Bacteria da Virus.

Amma da yake ana samar da Vitamin D a fatar mutum ne a lokacin da yake rana, mutane da dama suna da karancin sinadarin a lokacin hunturu.

Gwaje-gwaje da dama da mutane suka yi wajen yin amfanin da mangunan da zai samar da sinadarin Vitamin D domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka ya haifar da sakamako mai rudani.

Sakamakon hakan ne yasa masu binciken suka fito da kididdigar mutane 11,321 daga gwaje-gwaje daban-daban domin su samu kwakkwarar amsa.

Tawagar jami'ar Queen Mary da ke London, ta duba kwayoyin cututtuka da ke da alaka da sanyi, wadanda ke haddasa cututtuka kama daga kan mura zuwa ciwon sanyi.

Binciken ya ce mutum daya zai iya kubuta daga kwayoyin cuta a cikin ko wacce kwayar Vitamin D 33 da aka sha.

Hakan ya fi inganci a kan rigakafin mura, wanda ke bukatar sai an magance na mutum 40 domin kare mutum guda daga kamuwa da shi, duk da dai kamuwa da sanyi yafi azaba sosaifiye da murar da aka saba yi.

Mutanen da ke shan kwayar kullum ko kuma duk mako sun fi cin moriyarsa a kan wadanda suke sha duk wata da kuma ma wadannan da ma can suke da karancin sinadarin a jikinsu.

Me ya sa sinadarin Vitamin D ya ke da amfani?

Asalin hoton, BIOPHOTO ASSOCIATES/SCIENCE PHOTO LIBRARY

Bayanan hoto,

Wani sa'in rashin sinadarin vitamin D kan jawo yara su zama masu gwamiyar kafa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Muhimmin abin da ya ke yi shi ne gwada yawan sinadirin Calcium da na Phosphate da ke jikin mutum, wadanda ke da matukar amfani wajen inganta tare da kula da kasusuwa masu lafiya da hakora da kuma nama.

Wani sa'in rashin sinadarin vitamin D kan jawo yara su zama masu gwamiyar kafa, inda kasusuwan suke kasancewa ba su da kwari kuma sai su yi laushi.

Hakan kuma sai ya sauya suffar kasusuwan idan yaro ya ci gaba da girma.

A manya kuma, rashin sinadarin vitamin D na iya jawo tsananin laushin kasusuwa da rashin kwari wanda hakan ke jawo matsanancin ciwon jiki da na kasusuwa.

Amma kuma idan sinadarin Vitamin D ya yi yawa kuma zai iya jawo yawan sinadarin calcium a cikin jini wanda zai iya jawo matsalar zuciya da na koda.

Ya kamata duk wanda ya ke fama da wata cuta kuma yake shan magani ya nemi shawarar likitansa.

Masu bayar da shawara a kan motsa jiki sun bayar da shawarar cewa ya kamata mutane su rika shan sinadrin Vitamin D a lokacin kaka da kuma lokacin sanyi domin samun lafiya a kasusuwa da tsokar jiki.

Ana bai wa wadanda ba su samun isashen hasken rana a fatarsu shawarar su rika sha a ko da yaushe a cikin shekara.

Duk da haka, a na ta muhawara a kan muhimmancin binciken da aka yi na baya-bayan nan kan lamarin.