Pakistan: IS ta kashe gomman mutane a hubbaren Sufaye

'Yan sanda a Pakistan sun ce wani harin kunar-bakin-wake da mayakin kungiyar IS suka kai a hubbaren Sufaye da ke kudancin kasar ya yi sanadin mutuwar akalla 72.

Mutumin ya tayar da bama-baman da ke jikinsa a tsakiyar masu ibada a hubbaren wani Sufi mai suna Lal Shahbaz Qalandar a garin Sehwan na lardin Sindh, a cewar 'yan sandan.

Firai Ministan kasar Nawaz Sharif ya yi tur da harin, wanda tuni IS ta dauki alhakin kai shi.

Hare-haren da aka matsa kai wa a wannan makon sun wargaza dan zaman lafiyar da aka samu a kasar ta Pakistan.

Hubbaren cike yake da mutane a Alhamis ɗin nan saboda kallon da ake yi wa ranar a matsayin mai albarka.

Kungiyar samar da walwala ta Edhi Welfare Trust, wadda ta fi kowacce kungiya samar da motocin daukar marasa lafiya, ta ce maza 43 ne suka mutu, yayin da mata tara suka riga mu gidan gaskiya da kuma kananan yara 20.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya shaida wa BBC cewa akalla mutum 250 sun ji rauni sakamakon harin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kai wadanda suka jikkata wani asibiti
Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption An kai harin ne a wani hubbaren da ake girmamawa
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shirye-shiryen da aka yi a wani asibitin Karachi domin bai wa wadanda harin ya shafa agaji

Labarai masu alaka

Karin bayani