Me ya sa ake jayayya game da hankalin Donald Trump?

Donald Trump
Bayanan hoto,

A cikin wata wasiƙa, ƙwararru sun ce Donald Trump bai dace da zama shugaba ba

Ga alama, abin al'ajabi ne a tambayi mutumin da ke jagorantar kasuwancin biliyoyin daloli, wanda kuma ya kayar da gogaggun 'yan siyasa a takararsa ta shiga ofis mafi alfarma a Amurka, ƙoshin lafiyar iya kamun ludayinsa.

Amma ƙwararru suna muhawara a kan lafiyar ƙwaƙwalwar shugaban na Amurka.

Tattaunawa a kan lafiyar ƙwaƙwalwar Donald Trump ta fito fili ne saboda wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da wasu gomman ƙwararru suka rubuta cewa "gagarumin rashin nutsuwar shauƙinsa" ya sa bai dace da shugabancin ƙasa ba.

Kiran ga alama ya saɓa wa daɗaɗɗiyar al'adar ƙwararrun ta ƙin farraƙe batun lafiyar wani mutum-na-mutane, har ma wani babban likitan ƙwaƙwalwa ya yi tir da lamarin, ya ce "aibata lafiyar ƙwaƙwalwar" cin zarafi ne ga masu taɓuwa.

Me ya janyo haka?

Muhawara a kan ƙoshin lafiyar ƙwaƙwalwar Trump ba wani sabon abu ne ba, an fara hakan tun ma kafin zaɓensa a watan Nuwamban bara.

Sai dai mafi yawan ƙwararru kan lafiyar ƙwaƙwalwa sun ƙi fitowa su yi wa jama'a bayani, sakamakon wata ƙa'ida da suka kallafawa kansu mai suna "dokar Goldwater" wadda ƙungiyar masana lafiyar ƙwaƙwalwa ta Amurka ta amince da ita a 1973.

Ƙa'idar ta hana likitocin ƙwaƙwalwa farraƙe matsayin lafiyar wani, idan ba su ne da kansu suka duba shi ba. An ɗabbaƙa ƙa'idar ce bayan wata mujalla ta tambayi dubban ƙwararru a 1964 cewa ko ɗan takarar jam'iyyar Republican Barry Goldwater na da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa da zai iya shugabancin ƙasa.

Ƙungiyar likitocin dai ta yi gargaɗi a bara cewa keta dokar a wajen yin tankaɗe da rairaya kan lafiyar 'yan takara a zaɓen shugaban ƙasa "rashin sanin ciwon kai ne da yiwuwar nuna wa mutum tsangwama kuma tabbas ya saɓa wa ƙa'idar aiki".

Bayanan hoto,

Ana dai gargaɗin likitocin ƙwaƙwalwa game da canki-faɗi kan matsayin lafiyar ƙwaƙwalwar 'yan takara

Sai dai a yanzu wasu ƙwararru sun ɓara, ciki har da waɗnda suka sanya hannu a kan wani ƙorafi don cire Donald Trump. A yanzu ƙorafin ya samu sa hannun mutane fiye da dubu 23.

Wasu sun ce Mr Trump yana da larurar tsabagen nuna son kansa wato Narcissistic Personality Disorder (NPD).

A cewar mujallar Psychology Today, mutane masu irin wannan larura sau da yawa suna nuna wasu halaye kamar haka:

  • Gadara, rashin jimanta wa halin da wasu ke ciki da kuma son burga
  • Sun yi imani sun fi kowa ko kuma sun cancanci karramawa ta musammam
  • Tsabagen son burga da burgewa, ba sa jurewa suka ko faɗuwa

Mene ne sabo?

A cikin wata wasiƙa zuwa ga jaridar New York Times, Likitan ƙwaƙwalwa 35 sun yi gargaɗin cewa "gagarumin rashin nutsuwar shauƙin" da aka gani a jawabai da ayyukan Mr Trump ya sanya shi zama "wanda ba zai iya riƙe shugabancin ƙasa sannu cikin hankali ba".

Suka ce ƙwararru sun yi shiru da bakinsu ne saboda dokar Goldwater, amma yanzu lokaci ya yi da za su yi magana. "Wannan shirun ya janyo gazawa wajen ba da gudunmawar ƙwarewarmu ga 'yan jarida da 'yan majalisar da ke cikin damuwa a wannan muhimmin lokaci. Muna fargabar cewa akwai hatsari babba a ci gaba da yin shiru."

Bayanan hoto,

Wasiƙar ta ce Donald Trump ya nuna gazawa wajen nuna jimiri da ra'ayoyin wasu

Wasiƙar ta ƙara da cewa: "jawabi da ayyukan Mr Trump suna nuna gaza jimiri da ra'ayoyi daban da nasa, abin da ke janyo mayar da martani cikin fushi. Furuci da ɗabi'arsa na nuna gagarumar gazawa wajen jimantawa.

"Masu irin waɗannan halaye kan jirkita gaskiya ƙarara yadda za ta dace da yanayin tunaninsu, suna auka wa abubuwan da aka haƙiƙance a kansu da ma mutanen da ke tafe da su ('yan jarida da masana kimiyya)."

A farkon wannan mako, ɗan majalisar dattijai na jam'iyyar Dimokrat Al Franken ya ce "ƙalilan" cikin takwarorinsa na Republican sun bayyana damuwa a gare shi dangane da matsayin lafiyar ƙwaƙwalwar Mr Trump. Damuwar, a cewarsa, ta taso ne kan batun tsare gaskiyar shugaban ƙasar da kuma zargin cewa Mr Trump "ya cika ƙarya".

Me ya janyo taƙaddama?

Baya ga keta dokar Goldwater ƙarara da aka yi, wasu ƙwararru na cewa farraƙe matsayin lafiyar ƙwaƙwalwar Mr Trump wani cin zarafi ne ga masu taɓin hankali.

Haka zalika, a cikin wasiƙar da aka aika wa New York Times, Dr Allen Frances, wanda ya taimaka wajen rubuta Diagnostic and Statistical Manual of Mental Disorders IV, ɗaya daga cikin muhimman mujallun da ake amfani da su wajen rarrabe larurorin taɓuwar ƙwaƙwalwa, ya ce "mafi yawan likitocin duba lafiya 'yan jigari-jigari sun laƙaba wa" Mr Trump gwajin "larurar tsabagen nuna son kai".

"Yana iya zama mai son matuƙar kansa na nuna wa a duniya, sai dai hakan bai sa ya zama mai taɓin hankali ba, saboda ba ya fama da gigita da nakasar da ake nema don tabbatar da taɓin hankali ba."

Ya kuma ce: "Mr Trump ne kan haddasa (wa wasu) matsananciyar gigita maimakon a ce shi yake fama da ita kuma hakan ya biya shi matuƙa, maimakon shi ya gani a ƙoƙon shansa, saboda gadararsa, da nuna damuwa ga abin da ke gabansa kaɗai da kuma rashin jimantawa.

"Tsangwamar cin fuska ce ga masu taɓin hankali (waɗanda galibi ke da halin kirki kuma ba sa nufin sharri ga kowa) a yi musu kuɗin goro da Mr Trump.

"Rashin halin kirki a lokuta kaɗan ne yake zama alamar taɓin hankali, kuma a lokuta kaɗan ne masu taɓin hankali ke aikata abin tir. Aibata lafiyar ƙwaƙwalwa, bahagon tunani ne na ƙalubalantar matakin Donald Trump na far wa tsarin dimokraɗiyya."