Zuckerberg ya ce ana kafar-ungulu ga tsarin dunkulewar duniya

Mark Zuckerberg

Asalin hoton, AFP

Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ya bayyana matukar damuwa a kan kafar-ungulun da ake yi ga tsarin dunkulewar duniya wuri guda.

A wata hira da ya yi da BBC, Mr Zuckerberg ya ce labaran kanzon-kurege da ra'ayoyi masu raba kawunan jama'a da kuma irin bayanan da ake aikawa mutum ta shafukan zumunta bisa bayanan mu'amalarsa a intanet suna yin illa ga jama'a.

Ya kara da cewa bunkasar harkokin duniya ta sa an bar mutane a baya, lamarin da ya sa suke janyewa daga tsarin duniya na zama "tsintsiya madaurinki daya".

Ya ce "kada ku nade hannu ko ku yi fushi", a cewarsa kamata ya yi su taimaka wajen samar da "abubuwan jin dadin rayuwa".

Shugaban na Facebook ya ce , "A lokacin da na bude Facebook, burina shi ne na hada duniya wuri daya ta hanyar intanet ba domin na jawo ce-ce-ku-ce ba".

A cewarsa, "Kuma abin da yake faruwa kenan; ko wacce shekara duniya na ci gaba da dunkulewa wuri daya kuma kusan alkiblar da aka dosa kenan. Amma yanzu wannan batu na ci gaba da janyo takaddama."

Ya karaya

Mr Zuckerberg ya shaida wa BBC cewa : "Akwai mutane da dama a duniya da ke ganin an yi musu fintinkau a yunkurin dunkulewar duniya wuri daya da kuma sauyin da aka samu cikin sauri game da hakan, kuma hakan ya faru ne saboda wasu sun janye jiki daga shiga a dama da su."

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar nuna adawa da tsarin dunkulewar duniya kamar wannan a Philippines, sun fantsama ko'ina a duniya.

Wannan hira da aka yi da Mr Zuckerberg ta zo ne a daidai lokacin da ya wallafa wata wasika mai kalma 5,500 kan makomar Facebook da tattalin arzikin duniya.

A cikin wasikar, Mr Zuckerberg ya ambato tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln na yin bayani kan yadda za a ci gaba da kuma bukatar yin maraba da ra'ayin kowanne mutum, idan ba haka ba kuwa wasu za su yanke kauna ga duniya.

Kalubalen da duniya ke fuskanta

Da aka tambaye shi ko Shugaba Trump ya amince da ra'ayinsa cewa "hada mutane wuri guda" da kuma "dunkulewar duniya waje daya" zai kawo ci gaba, Mr Zuckerberg ya ce ba zai ce komai a kan hakan ba.

Ya dai ce, "Kuna iya tambayarsa kan hakan. Za ku iya yin nazari kan abubuwan da ya fada kan batun domin ku ware tsaki da tsakuwa".

Shugaban na Facebook dai bai halarci wurin taron da Mr Trump ya yi da manya-manyan kamfanonin fasaha na duniya ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mr Zuckerberg da matarsa Priscilla Chan sun kafa gidauniyar da ke bayar da tallafin jinkai

Mr Zuckerberg ya ce: "Daukacin kalubalen da muke fuskanta yanzu sun ta'allaka ne da dorewar duniya - yaki da sauyin yanayi da kawo karshen ta'addanci da cutuka da kuma kawo karshen yakin basasa a kasashen da ke yin sanadin kwararar 'yan gudun hijira cikin kasashe daban-daban ."

Asalin hoton, Getty Images