Nigeria: Sojoji sun yi artabu da mayakan BH

Boko Haram
Bayanan hoto,

A baya-bayan nan kungiyar na zafafa kai hare-hare bayan da a da sojoji suka kusa murkushe ta

A kalla mutum goma sha daya ne suka mutu, sannan wasu 17 suka jikkata a wani harin bam da aka kai bakin tashar motar Muna da ke birnin Maiduguri, a Arewa maso Gabashin kasar.

Ana zargin mayakan boko-haram da kai harin, inda 'yan kunar bakin-wake biyu suka mutu.

Mazauna birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya sun ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa uku da ake zargin bama-bamai ne a ranar Alhamis da daddare.

Bayani na nuna cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne da suka yi yukurin shiga birnin suka tayar da abubuwan, sai dai sojoji sun dakile yunkurin.

Ko da yake kawo yanzu babu cikakken bayanin asarar rayukan da aka samu daga hukumomi, wasu na fargabar an samu jikkata kuma wasu sun mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan Boko Haram din sun yi kokarin shiga Maiduguri ne ta Yerwa ta Custom House, sai dai ba su yi nasara ba.

Ganau da kuma sojoji sun ce mutane 11 ne suka ransu a yayin da mayakan Boko Haram din ke kokarin fatattakar 'yan kunar bakin wake a wajen birnin Maidugurin.

Bayanan hoto,

An kona tireloli kusan 11 dauke da kayayyaki a tashar Muna

Kamfanin dillanci labarai na AP ya ruwaito cewa 'yan kunar bakin wake tara da kuma fararen hula biyu ne wadanda suka mutu din.

Wannan artabu shi ne gagarumi da aka yi a 'yan watannin baya-bayan nan tsakanin Boko Haram da sojoji a birnin Maidugurin.

'Yan sanda sun ce 'yan kunar bakin wake uku mata sun sanya bam a wasu tireloli da ke tashar Muna da tsakar dare.

Bayanan hoto,

Motocin na dauke da kayan abinci da aka yi lodi don tafiya wasu garuruwa

'Yan kato da gora sun ce daga bisani sojoji suka bude wa wasu masu babura wuta wadanda su ne suka yi wa 'yan kunar bakin waken rakiya, inda aka kashe mutum shida cikin su.

Ga dai rahoton da abokin aikinmu Ibrahim Isah ya aiko mana daga wajen da lamarin ya faru a Maidugurin.

Bayanan bidiyo,

Yadda sojoji suka yi artabu da 'yan BH a Maiduguri

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da kungiyar ke yunkurin shiga birnin wanda tsohon hedikwatarta ne, amma aka dakile yunkurin.

Kungiyar ta Boko Haram kuma ta zafafa kai hare-haren kunar bakin wake a birnin a baya-bayan nan.