Mace ta zama gwamna a Masar a karon farko

Nadia Ahmed Abdou
Image caption Mace ta farko da ta zama gwamna a Masar

Nadia Ahmed Abdou ta zama gwamna a wani lardi na Masar, wanda hakan ya sa ta zama mace ta farko da ta dare wannan mukami a tarihin kasar.

An ranstar da Nadia a matsayin gwamnar Beheira ne, a yankin Nile Delta.

Nadia Abdou injiniya ce wadda aka sani da yin sosai a harkokin siyasar kasar, kuma ta kasance mace mai nuna iko wajen yanke shawara, inda har ake mata lakabi da, 'Mace mai kamar maza'.

Rahotonnin da jaridar Egypt Streets ta wallafa sun bayyana cewa, ta yi aiki a matsayin mataimakiyar gwamna tun shekarar 2013.

Nadia Abdou ta kuma shafe shekaru 10 tana aiki a matsayin shugaban kamfanin ruwan sha na birnin Alexandria, tsakanin shekarar 2002 zuwa 2012.

Labarai masu alaka