Gwamnatin Kenya ta musanta zargin leken asiri ta waya

Kenya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kenya ta musanta zargin leken asirin ul'ummar kasar

Hukumomi a Kenya sun fara wani shiri na sa-ido a kan hanyoyin sadarwa na wayoyin salula da kamfanonin sadarwa ke samar wa 'yan kasar.

Jama'ar kasar sun fara jin kishinkishin game da matakin ne ta hanyar wata wasika da aka kwarmata wacce ke cewa hukumar da ke sa ido a kan harkar sadarwa ta tilasta wa kamfanonin sadarwa lika wata na'ura ta leken asiri da ake kira Device Management System (DMS) a na'urorinsu.

An yi amanna ta hanyar wannan na'ura, gwamnati za ta iya karanta rubutattun sakwanni ta kuma kasa kunne a hirarrakin da mutane ke yi a wayoyinsu na salula.

Sai dai Darakta Janar na hukumar sadarwa ta Kenya, Francis Wangusi, ya musanta zargin na leken asirin mutane, yana cewa na'urar za ta taimaka ne wajen gano wasu na'urorin bogi da ake hadawa da wayoyin salula.

Amma 'yan kasar da dama, ciki har da masu fafutuka, sun yi amanna manufar shirin ita ce leken asirin al'ummar Kenya miliyan 30 wadanda suka mallaki wayoyin salula.

Wannan na'ura dai na iya fahimtar duk hirar da ake yi ta kuma gano abubuwan dake cikin wayar salula.