An hana amfani da 'yar tsana mai tonon silili a Jamus

Wata yarinya dauke da Cayla Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption A shekarar 2015 aka gano tawaya a manhajar da ke cikin 'yar tsanar

Wata hukuma da ke sa ido kan al'amura a Jamus ta yi kira ga iyaye a kasar cewa hana 'ya'yansu amfani da 'yar tsanar Cayla, saboda tana dauke da na'urar fasaha da ke iya bayyana wasu sirrikan mutane.

Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta kasar ma ta yi wannan gargadin.

Masu bincike sun ce masu satar bayanai za su iya amfani da na'urar Bluetooth da aka dasa a cikin 'yar tsanan domin ta saurara kuma ta yi magana da yaran da ke wasa da ita.

Har yanzu dai kamfanin samar da 'yar tsanar bai mayar da martani a kan gargadin da hukumomi suka yi ba.

A baya dai kamfanin Vivid Toy, wanda ke rarraba 'yar tsanar, ta ce masu satar bayanai ba su da damar da za su yi hakan kuma sai kwararru ne za su iya aikata hakan.

Duk da haka, ya ce kamfanin zai yi aiki da umarnin tun da zai iya kara inganta manhanjar da aka yi amfani da ita a 'yar tsanar.

Amma kwararru sun yi gargadin cewa ba a shawo kan matsalar ba tukuna.

Cayla tana iya amsa tambayoyin da masu wasa da ita suke yi mata ta hanyar tuntubar intanet.

Misali idan aka tambaye ta, 'Yaya ake kiran jinjirin doki? Sai 'yar tsanar ta ce ana, "kiransa Foal" a Turance.

Dama dai wasu 'yan kasar Amurka da kasashen Tarayyar Turai sun gabatar da korafe-korafe a kan haka.

Labarai masu alaka