'Yan jarida ba sa fadin gaskiya — Trump

An yi gangamin ne ranar 18 ga Fabrairun 2017

Asalin hoton, APTN

Bayanan hoto,

Donald Trump, ya ce, yana son tattaunawa da 'yan kasar ba tare da 'rairaye' abin da zai fada musu ba.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake kalubalantar gidajen jaridar kasar, in da ya bayana su da marasa 'fadin gaskiya' kuma masu 'son cimma burinsu', a lokacin wani gangamin magoya baya, a jihar Florida.

Mista Trump ya shaida wa taron cewa 'Yan jarida 'ba su so fadin gaskiya ba' kan zabensa sannan suna da 'ajendar da suke son cimma'.

Ya kuma kare muradun gwamnatinsa, a inda ya dage cewa yanzu haka suna kauraye kasar Amurka baki daya.

Da man dai shugaba Trump ya soki 'yan jaridar, yayin wani taron manema labarai, ranar Alhamis, sakamakon matsin lambar da gwamnatinsa take kara fuskanta.

Tun dai lokacin yakin zabensa da kuma bayan hawansa mulki, shugaba Trump yake samun rashin jituwa tsakaninsa da 'yan jaridar kasar.