Ina goyon bayan manufar Trump — Mugabe

Mugabe
Bayanan hoto,

Shugaba Mugabe shi ne ya fi ko wanne shugaba yawan shekaru a Afirka

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya ce yana goyon bayan shugaba Donald Trump kan manufarsa ta kare muradun Amurka da Amurkawa.

A jawabinsa na farko kan kamun ludayin mulkin Mista Trump, shugaba Mugabe ya ce ya yi mamaki kwarai da ya lashe zaben, duk da cewa dama ba ya goyon bayan 'yar takarar jam'iyyar Democrat Hillary Clinton.

Jaraidar Herald ta kasar ta ambato shi yana cewa, "In dai an zo batun shugaba Trump na kare muradun Amurka da Amurkawa, to na yarda da shi a nan. Mu ma burinmu shi ne mu kare muradin Zimbabwe da'yan kasar."

Ya kara da cewa ya kamata a bai wa Mista Trump dama don a ga salon kamun ludayinsa da kyau.

"Ban dai sani ba, amma ina ga ya kamata a bai wa Mista Trump lokaci, wata kila ma ya sake yin duba kan takunkuman da aka kakabawa Zimbabwe," inji Mista Mugabe.

Shugaban na Zimbabwe ya kuma ce shi zai ci gaba da mulkin kasarsa, don mutane da yawa sun yarda babu na biyunsa.

A ranar Litinin da daddare ne za a saki cikakkiyar hirar shugaban, gabannin bikin cikarsa shekara 93 a duniya, a ranar Talata.