Ana fama da yunwa a Sudan Ta Kudu

Matan da suka gujewa yaki a Sudan ta Kudu na bin layin karbar taimakon abinci, ranar 19 ga watan Oktobar 2016

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mutane na bin dogon layi don karbar taimakon abinci

An ayyana cewa ana fama da fari a wasu yankunan Sudan ta Kudu, karon farko da ba a samu irin haka a duniya ba tun shekaru shida da suka gabata.

Gwamnatin kasar da kuma majalisar dinkin duniya sun ruwaito cewa wasu mutum 100,000 na fama da matsananciyar yunwa, yayin da mutum miliyan daya kuma za su iya fuskantar fari.

ana zargin yaki da tabarbarewar tattalin arziki ne suka jawo lamarin.

An sha gargadin cewa za a a yi fama da yunwa a kasashen Yemen da Somaliya da Arewa maso Gabashin Najeriya, amma sai ga shi Sudan ta Kudu ce ta fara ayyana hakan.

A jihar Unity ce ake fama da yunwar, amma kungiyoyin ayyukan jin kai sun yi gargadi cewa za ta iya ci gaba da yaduwa idan ba a dauki matakin gaggawa ba.

Hukumomin agaji da suka hada da hukumar samar da Abinci da Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, sun ce mutane miliyan 4.9 - wato fiye da kashi 40 cikin 100 na al'ummar Sudan ta Kudu, na cikin tsananin bukatar abinci.

A yaushe ne ake ayyana yunwa?

A karkashin sharuddan Majalisar Dinkin Duniya karancin abinci na sanya mutane su rasa abinci mai gina jiki, amma ba a kowane lokaci ba ne hakan ke kaiwa ga yunwa ba.

Haka kuma samun tsawon lokaci ana fuskantar fari da sauran matsalolin da ke janyo karancin abinci ba lallai ba ne su janyo yunwa.

Ana ayyana yunwa ne idan aka samu mutuwar mutane tare da karancin abinci mai gina jiki kamar haka:

  • Akalla idan kashi 20 cikin dari na gidaje a yankin suna fuskantar matsanancin karancin kuma suka shiga cikin halin kaka-ni-kayi.
  • Idan matsanancin karancin abinci mai gina jiki ya wuce kashi 30 cikin dari.
  • Idan kuma mutuwar mutane ta wuce mutane biyu a rana a cikin mutane 10,000.

A ranar Litinin ne rahoton ya ce ana bukatar taimakon agaji domin kare yaduwar masifar yunwar a sauran sassan kasar.

"Idan har aka samu isasshen taimakon da ake bukata da gaggawa, to za a iya shawo kan matsalar nan da watani masu zuwa," inji rahoton.

Shugaban hukumar samar da abinci ta MDD a Sudan ta Kudu, Joyce Luma, ya ce yunwar - annoba ce da dan adam ya haddasa, bayan shafe shekaru uku ana yaki a kasar wanda ya yi mummunan tasiri ga harkar noma.

Rahoton ya kara da cewa, "Masifar yaki da tsadar kayan abinci da tabarbarewar tattalin arziki da rashin amfanin gona su ne musabbabin jawo matsalar yunwar."

Ba wannan ne karo na farko da Sudan ta Kudu ta fuskanci wannan matsala ba. A shekarar 1998 ma a lokacin da aka kasar ta yi yakin neman 'yanci daga Sudan, ta sha fama da yunwa.

A makon da ya gabata ne hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa fiye da mutane miliyan 20 na iya fuskantar yunwa a kasashe daban-daban nan da watanni shida.