An sa dokar hana mata bulaguro ba muharrami a Libya

Matan Libya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fuad Gritli wani mai barkwanci dan kasar Libya mazaunin Jordan ya yi wata sabuwar waka a kan lamarin

An sanya wata doka mai cike da ce-ce-ku-ce a Libya, ta hana mata 'yan kasa da shekara 60 a Gabashin kasar yin bulaguro.

Shugaban rundunar sojin kasar Abdul Razzaq Al-Naduri, ne ya sanya wannan dokar.

Umarnin ya hada da haramta musu hawa jr=irgi don tafiya wata kasa su kadai ba tare da muharrami ba a filin jirgin saman Labraq da ke Kudancin kasar.

A karshen makon da ya gabata ne dokar ta fara aiki kuma ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta a tsakanin 'yan kasar, wadanda ke sukar umarnin.

Fuad Gritli wani mai barkwanci dan kasar Libya mazaunin Jordan, ya yi wata waka a kan lamarin.

Jami'ai dai sun ce an dauki matakin ne saboda dalilan tsaro, kuma sun musanta cewa addini ne yasa suka yi hakan.

Sun kara da cewa hukumomin leken asirin kasashen waje na amfani da matan kasar da ke yawan tafiye-tafiye don wakiltar kungiyoyin fararen hula.

Saudiyya ta haramta wa mata yin bulaguro ba tare da muharramansu ba, inda suke kafa hujja da shari'ar Musulunci, duk da cewa wasu ba su yarda da hangen nasu ba.

Hana mata 'yan kasa da shekaru 60 yin bilaguro na baya-bayan nan ba tare da muharraminsu ba, ya shafi matan da ke Gabashin kasar ne kawai.

Hakan yana nuna bambancin siyasar da ake ta samu a Libya wanda ke neman raba kasar biyu, inda ko wanne bangare yake son saka dokokinsa a yankin da yake da iko.