Tamaula: Masar ta tabbatar da hukuncin kisa kan mutum 10

Kusan shekara hudu kenan da rikicin na Port Said

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kusan shekara hudu kenan da rikicin na Port Said

Babbar kotun daukaka kara ta Masar ta jaddada hukuncin kisan da ta yankewa wasu mutane 10, sakamakon wata tarzoma da aka yi a shekarar 2013, wacce ta yi sanadin mutuwar sama da mutane 70.

Rikicin wanda 'yan kasar ke kira da 'Kisan kiyashin Port Said', ya faru ne bayan kammala wasan kwallo tsakanin manyan kungiyoyi biyu masu adawa da juna.

Magoya bayan kungiyar al Masry wadda aka yi wasan a gidanta, sun far wa magoya bayan kungiyar al Ahly da ta ziyarce su, inda aka kashe wasu, aka yi wa wasu dan banzan duka tare da tattake wasu har suka mutu.

An yi ta Allah-wadai da 'yan sanda da rashin yin abin da ya dace don tsayar da rikicin, har ma wasu ke ganin jami'ai ne suka rura wutar rikicin sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan tumbuke Hosni Mobarak daga kan mulki.