Hikayata ta kawo sauyi a adabin Hausa

Ranar Lahadi ne masu sauraren Sashen Hausa na BBC a rediyo suka ji na karshe a jerin labarai goma sha biyun da suka cancanci yabo a bisa ma'aunin alkalan gasar kagaggen labari ta mata zalla ta BBC Hausa, wato Hikayata.

An dai zabo wadannan labarai ne, da ma ukun da suka lashe gasar, daga cikin labarai fiye da 200 da aka shigar gasar daga sassan daban-daban na duniya.

Labaran dai sun yi magana a kan batutuwa da dama da suka shafi mata, kama daga zaman aure zuwa ga taka rawa a harkar ci gaban al'umma.

Malama Rahama Abdul Majid fitacciyar marubuciya ce, kuma mai sharhi a kan adabin Hausa; sannan tana cikin alkalan gasar ta Hikayata.

A wata hira da ta yi da Muhammad Kabir Muhammad ta yi bayani a kan jigon gasar.