Kashi 80% na giwayen Gabon sun kare

Giwayen Afirka sun tasar wa karewa
Bayanan hoto,

Ana yawan farautar giwaye a Afirka

Yawan giwayen da ake da su a nahiyar Afirka na barazanar karewa sakamakon farautarsu da ake yawan yi.

Wani sabon rahoto ya ce Gabon ta rasa kashi 80 cikin 100 na giwayen kasar, cikin shekara 10 da ta gabata.

Masu bincike sun ce mafarautan da suke shiga kasar daga Kamaru, sun kashe mutane da dama kan neman hauren giwa.

Dama kasar Gabon ce wadda ta rage mai yawan giwaye a dazukanta a Afirka.

Amma masu bincike daga jami'ar Duke da ke Amurka, sun ce an yanka kusan giwaye 25,000 a gandun namun daji na Minkebe, wani waje da ake dauka mai aminci.