An kafa dokar hana fita a kudancin Kaduna

Kaduna

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Rikicin kudancin Kaduna na janyo cece-kuce a Najeriya

Majalisar tsaron ta jihar Kaduna a Najeriya ta ayyana dokar ta-baci a kananan hukumomi biyu a kudancin jihar domin kwantar da wani sabon rikicin da ya barke a can.

Wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar, Samuel Aruwan, ya fitar ta ce an umurci jami'an tsaron da ke kananan hukumomin Jama'a da Kaura su aiwatar da dokar.

Kwamandan rundunar sojin Najeriya na daya da kuma kwamishinan 'yan sandan jihar sun koma kudancin jihar sakamakon sabbin hare-haren da aka kai yankin.