EU ta kakaba wa Mugabe sabbin takunkumi

Shugaba Mugabe

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Mugabe shi yake mulkin Zimbabwe tun bayan kasar ta samu 'yancin kanta.

A daidai lokacin da shugaba mafi yawan shekaru a duniya, Robert Mugabe na Zimbabwe, ya cika shekara 93, Tarayyar Turai ta kara kakaba masa sabbin takunkumi.

Matakin zai hada da takaita tafiye-tafiye, da hana amfani da kadarori da kuma hana cinikayyar soji tsakanin kasashen kungiyar Tarayyar Turan da shugaba Mugabe da matarsa Grace da kuma bangaren tsaron kasar.

Amma, majalisar Tarayyar Turai ta kada kuri'ar dage takunkumin makamai na wucin gadi. Za ta bari a shigar da abubuwan fashewar da ake amfani da su wajen hakar ma'adinai da samar da ababaen more rayuwa a kasar tukunna.

Za'a sake duba takunkumin badi.

Tarayyar Turai ta fara kakabawa Mugabe takunkumi ne a shekarar 2002 bayan an far wa gonakin fararen fata, da magudin zabe da kuma cin zarafin babbar jam'iyyar adawa da kuma masu fafatukar 'yancin dan adam.

Shugaba Mugabe ya ce takunkumin ya janyo wahala ga mutanen kasar, kuma daya ne daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Birtaniyya na son ganin ta tumbuke shi daga mulki.

A ranar Talata da shugaba Mugabe ke cika shekara 93 a duniya, dukkan jaridun kasar sun yi ta taya shi murana har ma da jaridun da aka san su da nuna adawa da shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga 'yan kasar da su daina bautawa Turawa, su zama masu tunanin neman na kansu don tallafawa tattalin arzikin kasar.