Azerbaijan: Shugaban kasa ya nada matarsa mataimakiya

Ilham Aliyev

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A bara kasar ta samar da sabon matsayin a wani bangare na jeri sauye-sauye da Ilham Aliyev a kundin tsarin dokar kasar

Shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev, ya nada matarsa Mehriban, a matsayin mataimakiyar shugaban kasa ta farko.

A bara ne dai aka samar da gurbin wannan matsayin a jerin sauye-sauyen da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar.

Mehriban Aliyeva dai 'yar wata zuria'a ce ta masu karfin iko a kasar.

Ta yi karatun likita, amma kuma yanzu ita ce shugabar gidauniyar Heydar Aliyev, wadda aka samar domin tunawa da mahaifin mijinta.

Mahaifin mijin nata shi ne tsohon shugaban hukumar tsaro ta KGB, kuma shi ya jagoranci kasar shekara da shekaru.

Mehriban Aliyev dai 'yar majalisar kasar ce.

A shekarar da ta gabata ne dai wasu bayanan sirri na diflomasiyyar Amurka da aka sake, suka gano cewar duk da 'yar majalisa ce, matar shugaban kasar ba ta da cikakken sani a kan al'amuran siyasa.