'Yan majalisa sun amince da noman tabar wiwi a Netherlands

'Yan kasar Netherlands sun amince a sayar da tabar wiw maras yawa

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

'Yan kasar Netherlands sun amince a sayar da tabar wiw maras yawa

Majalisar wakilan Neitherlands ta amince da noman tabar wiwi a kasar.

Wani kudurin doka da aka amince da shi a zauren majalisar zai hana a yi hukunci kan wadanda suka kware kan noman wiwi, koda yake za a sanya musu sharudan noman.

Sai dai wannan kudiri ba zai zama doka ba, har sai 'yan majalisar dattawa sun amince da shi.

Sayan tabar wiwi a kantunan sayar da gahawa dai ba laifi ba ne a kasar ta Neitherlands, amma sayarwa masu kantinan gahawar babban laifi ne.

Irin masu wadannan kantuna dai kan samu tabar wiwin ne daga hannun masu aikata muggan laifuka.

Wani dan majalisa a karkashin jam'iyyar Liberal D66 shi ne ya gabatar da kudurin dokar, wanda tuntuni yake goyon bayan matakin.

'Yan majalisar 72 cikin 77 ne suka kada kuri'ar amincewa da sabuwar dokar, duk da cewa jama'a sun nuna damuwa kan halatta noman wiwin, da suka ce zai sanya Neitherlands take dokokin kasashen duniya.

Sashen kula da lafiya na kasar ya nuna damuwa kan matakin, duk da cewa babu tabbas kan amincewa da shi a majalisar dattawa amma wadanda suke saye da sayar da wiwi sun yi maraba da kudurin.

Shugaban kantunan sayar da gahawa na kasar Joachim Helms, ya ce idan har majalisar dattawa ta amince da sabon kudurin dokar, wannan labari ne da zai dadadawa masu sayar da gahawa rai.