Auren jinsi daya ya sa yara sun rage kashe kansu a Amurka

Fadar White House ta dauki launin bakan gizo, bayan kotun kolin Amurka ta amince da dokar a shekarar 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An dai dauki shekara 17 ana gudanar da binciken, har zuwa lokacin da kotun koli ta ayyana 'yancin auren jinsi guda

Wani bincike da aka gudanar, ya gano an samu raguwa matuka kan yunkurin hallaka kai tsakanin 'yan makaranta matasa a Amurka, tun bayan amincewa da auren jinsi daya.

Masu binciken sun ce an samu raguwar yunkurin hallaka kai da kashi bakwai cikin dari bayan shafe shekara 17 ana gudanar da binciken.

Binciken ya ce dokokin amincewa da auren jinsi guda suna yin tasiri ga yanayin aikin kwakwalwar mutane.

Sai dai rahoton ya ce kai-tsaye ba za a ce ga takamaimai adadin yawan matasan da auren jinsi guda ya tserar daga hallaka kan su ba.

Amma hallaka kai na daga cikin sanadiyyar mutuwar matasa daga shekara 15 zuwa 25 a Amurka.

Haka kuma cikin kashi 29 cikin 100 na dalibai 'yan luwadi, da madigo da masu aikata duka abubuwa biyun, sukan yi yunkurin hallaka kan su cikin shekara guda gabanin fitar da rahoton.

Sabon rahoton ya kara da cewa binciken da aka gudanar da jihohi 32 na Amurka, wadanda suka amince da auren jinsi guda, ya gano an samu raguwa na yawan matasan da suke kashe kan su idan aka kwatanta da lokutan baya.

Haka kuma an samu karuwa a jihohi 15 din da ba su amince da auren jinsi daya ba.

A karshe jagoran binciken Julia Raifman ta ce, abin sha'awa ne a zo lokacin da 'yan luwadi, da madigo, suka rage hallaka kan su.

Ta kara da cewa ta yiwu samun 'yanci na daga cikin dalilan da suka sanya aka samu wannan sakamakon.