Trump ya fitar da sabbin ƙa’idojin korar baƙin-haure

A US Border Patrol agent looks on at people along the US-Mexican border.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

The memos expand the number of undocumented immigrants subjected to deportation

Gwamnatin Donald Trump ta fitar da wasu sababbin tsauraran ƙa'idoji wadanda za su sanya a hanzarta korar baƙin-haure daga Amurka.

Ka'idodjin za su tabbatar cewa an kori mutanen da ba su da takardun izinin zama a kasar idan sun karya dokokin hanya ko kuma suka yi sata a kantuna kamar yadda ake yi wa wadanda aka kama da aikata manyan laifuka.

Ka'idojin ba su yi karan-tsaye ga dokokin shige-da-fice na kasar ba, sai dai za su tsananta kan aiwatar da hukunce-hukunce.

An yi kiyasin cewa akwai baƙin-haure miliyan 11 a Amurka.

A ranar Talata, kakakin fadar White House Sean Spicer ya ce sababbin ka'idojin ba za su sanya a fitar da baƙin-haure da dama lokaci guda ba, yana mai cewa an tsara su ne domin su karfafa wa jami'an tsaro tabbatar da dokokin da ake amfani da su.

A cewarsa,"Sakon da fadar White House da kuma ma'aikatar tsaron cikin gida ke son aikewa shi ne mutanen da ke zaune a kasar na, wadanda ke yi mata barazana, su za su fara ficewa daga cikinta."

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jami'an shige-da-fice sun kulle wani bakon-haure a Los Angeles a wannan watan.

Wasudaga cikin sabbin ƙa'idojin: