'Yan siyasa irin Donald Trump sun raba kan duniya - Amnesty

President Donald Trump gesture as he walks on the South Lawn on 20 February

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Amnesty ta ce Mr Trump ya yi kalaman da ke tayar da hankali

Amnesty International ta ce 'yan siyasar da ke yin amfani da kalaman raba kawuna suna jefa duniya cikin mummunan hatsari.

A rahotonta na shekara-shekara, Amnesty ta ce mutane irin su Shugaba Donald Trump na cikin misalan 'yan siyasar da suka sanya ake mayar da fagen siyasa tamkar "na kyama da raba kan jama'a".

Rahoton ya kuma caccaki shugabannni, cikin su har da na Turkiya, Hungary da kuma Philippines, wadanda rahoton ya ce sun yi kalamai da ke jefa tsoro da kuma tsana har ma da raba kawunan jama'a.

Kungiyar ta Amnesty ta ce 'yan siyasa na yin amfani da batun 'yan gudun hijira domin neman farin jini a tsakanin al'umomin kasashensu.

Rahoton, wanda ya yi nazari kan kasashe 159, ya bayyana cewa ana yi kalaman da ke nuna kiyayya a Amurka da Turai a kan 'yan gudun hijirar musamman game da jinsi da da launin fatarsu da kuma addininsu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Amnesty ta soki yadda kasashen duniya suka tafiyar da rikicin Syria

Asalin hoton, Reuters/AFP

Bayanan hoto,

Mr Duterte na Philippines, Mr Erdogan na Turkiyya da kuma Mr Orban na Hungary na cikin shugabannin da suka sha suka daga Amnesty