Me ya sa ake son yin dokar hana 'talaka futuk' aure da yawa?

Brides at a mass wedding held in Kano, Nigeria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sarkin yana son ya yi garambawul ga fannonin dokar aure.

Auren mace fiye da daya wata al'ada ce wadda ta samu karbuwa a Najeriya, amma wani shugaban addinin Musuluncin kasar yana so a yi dokar da za a dinga hakan kan tsari.

Me yasa ake son yin dokar hana auren mata da yawa?

Ana son yin wannan doka ne saboda irin yadda mazan da ba su da karfin daukar nauyin mace fiye da daya amma suke yin hakan.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce auren mace fiye da daya ga mara sa galihu, ba shi da fa'ida tun da mutum ba zai iya kare hakkokin da Allah ya dora masa ba.

Al'amarin da ka iya jawo a haifi yara a bar su sakaka ba tarbiyya har su shiga wani hali na munanan dabi'u kamar ta'addanci da sauran su, inda a yanzu ma ake fama da matsalar tayar da kayar baya daga kungiyar Boko Haram.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Boko Haram ta kai hare-hare Kano

Kungiyar ta samu nasarar jan ra'ayin dumbin matasa daga Arewacin kasar.

"Mu da ke Arewa mun ga irin fadi-tashin da mazan da ba su da karfin auren mace fiye da daya amma suke auren mata hudu ke fama da shi"

"Za su haifi 'ya'ya 20, wadanda ba za su iya basu ilimi ba. Za su bar su a kan titi. Kuma yaran za su zama 'yan daba ko 'yan ta'adda," inji Sarki Sunusi.

Wadansu masu sharhi na ganin wadannan kalaman na Sarki lallai babu tantama a kansu in har mutum ya san yadda Arewacin kasar yake.

A akasarin garuruwan da ke Arewa da kuma birane, za a dinga ganin yadda almajirai suke karakaina a kan tituna suna bara, wadanda iyayensu ke tura wa garuruwa da sunan karatu.

Auren mace fiye da daya ya zama ruwan dare?

'Yan bokon Arewacin Najeriya, ba su cika yin auren mace fiye da daya ba, amma hakan ya zama ruwan dare a tsakanin mutanen karkara da kuma wadanda ake gani "a marasa karfi."

Bayanan hoto,

Mohammed Bello Abubakar Masaba ya mutu ya bar mata sama da 100

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Addinin Musulunci ya yarda da auren mace daga daya zuwa hudu, sai dai malamai da dama sun ce, 'addinin bai halatta hakan ba, sai da ya sanya sharudda da ake ganin in har mutum bai cika su ba, to barin auren mace fiye da dayan shi ya fi masa alkhairi.'

A wani lokacin ma a kan samu mutane sun wuce ka'idar da addinin ya shimfida musu, kamar yadda aka taba samun wani mutum a jihar Neja da ke yankin tsakiyar Najeriya, wanda ya mutu a watan da ya gabata, ya taba auren auren mata sama da 100 ya kuma haifi 'ya'ya 113.

Amma shari'ar Musdlunci ba ta yarda da auren mace sama da hudu ba, a don haka ne Alhaji Mohammed Abubakar Masaba, ya sha suka daga wajen 'yan kasa da malaman addini.

Ko a dokar Musulunci shi kansa auren mata hudun 'Sai idan mutum zai iya adalci a tsakanin iyalan nasa,' wanda malamai suka yi bayanin cewa adalcin ya hada da iya ciyar da su, da tufatar da su, da ba su ilimi da kuma ba su muhalli.

Shin hana aure da yawa ba bisa tsarin shari'a ba zai rage samun yara marasa tarbiya?

Baya ga cewa Sarkin Kano ya dogara ne da hujjojin shari'ar Musulunci da ke nuni da cewa, kar mutum ya yi abin da ya san ba zai iya sauke hakkinsa ba, kamar auren mata da yawa a haifi 'ya'ya a kasa ba su tarbiyya, to shi ma wani binciken da aka buga a mujallar Royal Scientific a shekarar 2012, ya ce an fi samun yawan fyade da yake-yake a al'ummar da ake auren mata fiye da daya ba tare da basu hakkokinsu ba.

Matsalar ba wai kawai ta ta'allaka ba ne a kan yaran da ake barin su sakaka ba ilimi da tarbiyya, har da ma yawan matasa marasa hali da ba su da halin aure.

Ya ya za'a kaddamar da dokar?

An mika shawarar ga wata majalisar malaman addinnin Muslunci domin su rattaba hannu a kanta, sannan a mika ta ga majalisar dokokin jihar Kano nan da mako biyu.

Idan har aka amince da zamowarta doka, to za'a aiwatar da ita ne a kotun Musulunci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sarki Sunusi yana da karfin fada aji

Kano na daya daga jikin jihohi bakwai da suka kaddamnar da shairi'ar Musulunci a shekarar 1999 - Kuma kotun Musluncin tana aiki ne a wasu lokutan da kotun kundin tsarin mulkin kasar.

A Kano a kan yi duk wata shari'a da ta shafi zamantakewar iyali ne a kotun Musulunci.

Amma matsalar ita ce a Najeriya ba a faye yin rijistar aure a wajen gwamnati da kuma kotu ba.

Shin wasu jihohin za su bi sahun Kano?

Shawarar za ta yi aiki a Kano ne kawai, amma Sarkin yana da karfin fada a ji, kuma akwai yiwuwar za'a iya daukar salon a wasu jihohin da ke amfani da shari'ar Musulunci.

Kudurin na daya daga cikin garambawul din da Sarki Muhammadu Sanusi ke fatan yi domin ciyar da arewa gaba, wadda ke bayan Kudancin kasar ta fannin tattalin arziki da kuma karatu.

Me ye sabo a wannan doka?

Kudurin zai kuma kunshi sauran hakkokin aure da karatu da kuma rabon gado.

Zai haramta cin zarafin abokan zama a gidan aure, da bai wa mata damar neman diyya kan duk wani zalunci da aka yi musu kamar na duka, da kuma damar neman saki idan har ana gallaza musu a zaman aure kuma suka ga cewa sun gaji.

An haramta cin zarafin mata a Najeriya, amma kamar yadda wani lauyan iyali IK Nwabufo, ya ce, "Raunin da wasu mutane ke da shi" na hana tabbatar da wadannan dokokin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mata masu ilimi a jihar Kano na tsakanin kashi 35 zuwa 50 cikin dari

Masu fafutuka na ganin yawancin fannonin shari'ar kasar daga ofishin 'yan sanda zuwa kotu, wurare ne da maza suka fi rinjaye, kuma ba a cika mayar da hankali kan shari'un zamantakewar aure don a kwatowa wanda ake zalinta hakki ba.

"Abin da sarkin ke son yi shi ne rage irin wadannan rashin bayar da hakki," inji Mista Nwabufo.

Ya kara da cewa, "Yana kokarin ya tabbatar da cewa kotunan shari'ar Musuluncin suna yin hukunci ne kan tsarin da Musulunci ya tanada, ba yin duba ga al'adu ba."

Dokar za ta kuma hana auren dole ga mata.

Amma akwai inda hakan bazai yiwu ba-- misali idan Baban yarinya zai iya tabbatar da cewa tana da tabin hakali da takardun asibiti, to zai iya yanke hukuncin yi mata aure da wanda ya zaba mata..

Masu sharhi da dama a shafukan sada zumunta da muhawarar kasar, sun yi ta rubutu kan cewa, "Ganin yadda matakin ilimi ke yin kasa sosai a Arewacin kasar - musamman ma ga mata- da wuya akasarin mata su gane gatan da dokar take son yi musu."

Matan Sarki Sunusi nawa ne?

Sarkin yana da mata hudu, kuma ya ce babu laifi idan mutum ya auri mace fiye da daya idan har zai iya yin adalci tsakaninsu kuma zai iya daukar nauyinsu da 'ya'yansu.

"Amma da alama yana son al'ummar Kano su dinga yin abin da ainihin shari'a ta tsara ne kan zamantakewar aure," inji Abubakar Abu Humaida, wani mai bayyana ra'ayinsa a shafin Facebook.

Kafin ya zama sarki, mai martaba wani sanannen mutum ne - wanda ya taba aikin banki har ma ya rike matsayin gwamnan babban bankin Najeriya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sarkin ya fallasa cin hanci da rashawa a lokacin da yake shugaban babban bankin Najeriya

Ya yi shugabancin babban bankin Najeriya a lokacin a mulkin shugaba Goodluck Jonathan, a lokacin da ya kwarmata bayani kan badakalar cin hanci da rashawa a bangaren man fetur na kasar.

An cire shi daga mukamin saboda ya fito ya yi magana.

A makon da ya gabata ma, ya yi wani jawabi a wajen wani taro inda ya bayar da shawara cewa a mayar da mafi yawan masallatan Arewacin kasar zuwa makarantu, a ganinsa ba za a iya cikakkiyar ibada ba tare da ingantaccen ilimi ba.

Ya koka kan koma bayan da bangaren ilimi ke fuskanta a Arewacin kasar, har ma ya ba da misali da yadda kasar Moroko ta ci gaba ta fuskar ilimi.

Amma ana ganin kalubalantar wadansu al'adu da aka dade ana yi a Arewacin kasar zai yi wuya, duk da cewa idan aka dubi fuskar addini za a samu ba haka ainihin tsarin yake ba.