Kiran AU ta kare 'yan Nigeria shirme ne — Afirka ta Kudu

South Africa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya ta ce an kashe 'yan kasar kimanin 116 tun shekara biyun da suka wuce a Afirka ta Kudu

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi fatali da kiran da Najeriya ta yi ga kungiyar Tarayyar Afirka da ta kare 'ya'yanta mazauna can.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Afirka ta Kudu ta kuma yi fatali da ikirarin Najeriya cewa an kai wa 'yan kasar harin kyamar baki.

Mai magana da yawun ma'aikatar Clayson Monyela, ya ce hare-haren kyamar baki ba wani abu ba ne face laifin da ake aikatawa nan da can.

Gwamnatin kasar ta Afirka ta Kudu ta kara da cewa tayar da jijiyar wuyan da 'yan Afirka ta Kudu da 'yan kasashen waje ke yi a kafafen sada zumunta ba shi da amfani.

Yawan sakwannin barazanar da ake wallafawa a shafukan sada zumunta ya karu tun bayan hare-haren da aka kai a kan gidaje da kuma shagunan baki kusa da Johannesburg da Pretoria.

A karshen makon jiya ne dai aka wawushe, sannan aka kona shaguna 30 na baki a wadansu unguwanni a Pretoria, lamarin da ya sa hukumomin Najeriya suka yi kira ga Tarayyar Afirka da su dauki matakin kare 'yan Najeriya a can.

'Zanga-zanga a Najeriya'

A ranar Laraba ne kuma majalisar matasa ta Najeriya ta gudanar da wata zanga-zangar lumana a kofar ofishin jakadancin Afirka ta Kudu da ke Abuja.

Matasan sun yi zanga-zangar ne domin nuna kin amincewa da yadda ake kashe wasu 'yan kasashen Afirka da ke zaune a Afrika ta Kudu ciki har da 'yan Najeriya.

Bayanan hoto,

'Yan Najeriya sun yi zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Afirka ta Kudu a Abuja

Matasan sun mika wa jakadan Afirka ta Kudu takardar koke don jan hankalin kasarsa ta dauki matakin gaggawa domin dakatar da hare-hare da kashen-kashen da ake yi wa bakaken fata 'yan Afirka.

A shekarar 2015 ma an samu irin wadannan hare-hare na kin jinin baki a Afirka ta Kudu, inda aka kashe mutane tare da kona wuraren sana'arsu.

Babbar mai bayar da shawara ga shugaban Najeriya kan al'amuran da suka shafi 'yan kasar a kasashen ketare, Abike Dabiri, ta ce an kashe 'yan Najeriya da dama a Afirka ta Kudu shekara biyu da ta gabata, kuma mafi yawansu an yi musu kisan gilla ne.