'Ilimi ya tabarbare a Niger'

Shugaba Mahamadou Issoufou

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Gwamnatin Mahamadou Issoufou, tana son farfado da ilimi a Jamhuriyar Niger.

Wani bincike da ma'aikatar ilimi a Jamhuriyar Niger ta yi, ya nuna cewa ilimi ya tabarbare a kasar inda mahukunta ke cewa malaman makaranta ma ba su da ilimin da ya kamata su samu kafin su fara koyarwa.

Ministan Ilimin firamaren kasar, Dakta Mammadu Dauda Marta, ya ce suna son su tantance wadanda ke koyarwa a kasar inda ya ce za a tabbatar malaman sun iya koyarwa.

Ya kara da cewar gwamnatin kasar tana son dawo da martabar ilimi a kasar nan da shekara biyar ko goma.

A watan Maris mai kamawa ne ake ganin za a fara yi wa malaman bitar, inda gwamnati da iyayen yara ke ganin hakan zai taimaka wajen magance wasu daga cikin matsalolin ilimin kasar.